Bisa nakaltowar wakilin Kamfanin
dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya kawo maku rahoton daga
Karbala Mu’alla, Uwargidan Shaikh Zakzaky da wasu mata ‘yan Najeriya da suka zo
Karbala domin gudanar da aikin ziyarar Arbaeen din Imam Husaini As, sun gana da
Ayatullah Riza Ramazani, babban sakataren Majalisar Ahlul Baiti As ta duniya.
A cikin wannan ganawar an gabatar da rahoto kan sabbin ayyukan zamantakewar mata 'yan Shi'a a Najeriya tare da bayyana buri da kaunar da al’umma ke yi na son sanin koyarwar Ahlul-baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su.
A cikin wannan ganwar, Ayatullah Ramazani, ta hanyar karramawa da jinjinawa mujahida Uwargidan Shaikh Zakzaky wajen reno da tarbiyyar yaranta shahidai da kuma kyakkyawar alakarta ta kasancewa tare da Shaikh Zakzaky, ya bayyana cewa: Kamar yadda Shaikh Zakzaky ya ke kai, wajen gabatar da Mazhabar Ahlul Baiti mu nisanci wuce gona da iri da bayyana koyarwar Ahlul Baiti As.
Ya bayyana cewa Musulunci da mazhabar Ahlul Baiti sun yi daidai da dabi'ar dan Adam kuma muna da kyakkyawan fata a nan gaba.
A yayin da yake jawabi ga uwargidan Shaikh Zakzaky, Ayatullah Ramazani ya ce: Muna alfahari da ke da Sheikh da kuma iyalanku, kuma muna farin ciki da cewa gaba daya yanayinku duka biyun ya yi kyau.
