23 Agusta 2024 - 11:44
Bidiyon Yadda Ake Sauke Ruwan Sha A Maukibi Mai Lamba 1 Na Gidauniyar Ashura International Foundation

A yanzu haka (ranar Juma'a 2 ga Shahrivar 1403) wanda yayi daidai da 23/08/2024 an sauke wani sabon kwalayen ruwan sha a cikin maukibi mai lamba 1 da ke kan titin al-Baroudi a Karbala, Mu'alla.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya habarta maku cewa: Ya kamata a lura da cewa maukibin gidauniyar suna ba da hidimar al'adu da jin dadin jama'a – masu tattakin Arbaeen, kamar amsa tambayoyin addini, nasiha, rarraba litattafai na yara da na aikin Ziyarar Arbaeen a cikin harsunan Larabci da Farisanci, Intanet kyauta, rarraba tutoci masu alaka da Arbaeen, sanyaya da hutawa da shayarda ruwa, rabon abinci Da... suna masu hidimtawa ga masu ziyarar Arbaeen Husaini.