Iyalan babban malamin sun samu ganawa da jagoran harkar musulunci a Nigeria Hassan Adamu Tsoho, yana ɗaya daga cikin Ƴaƴan Marhum Sheikh Adamu Tsoho Jos, a yayin da ya miƙawa jagora littafin da mahaifiyarsu ta Buga Hadiyya ga Ruhin Sheikh Adamu Tsoho. Littafin an raba shi ne a wajen addu'a Addu'a cika kwanaki Bakwai (7) na rasuwar Sheikh Adamu Tsoho.
Bangon Littafin ta gaba Hotunan Marhum Sheikh Adamu Tsoho ne guda Biyar ciki harda hoton Mahaifin Sheikh Adamu Tsoho wato Alhaji Ahmed Tsoho Kifa da kuma na Marigayiya Muslima Adamu Tsoho. A bayan littafin kuma hoton Marhum ɗin ne guda ɗaya sai taƙaitattun zantukansa da yayi na nasihohi akan mutuwa.
Cikin littafin addu'oi ne wanda ya haɗa da Du'aul Khumayl, Du'aul Jaushanul Khabeer, Du'aul Tawassul, Du'aul Nudba, da sauran addu'oi daga cikin Littafin Mafatihul Jinan. An buga littafin ne aka raba da nufin Allah ya kai lada ga Ruhin Marhum Sheikh Adamu Tsoho Jos, kuma ana so duk wanda ya karanta ɗaya daga cikin addu'oi da littafin ya karanta "Kulhuwallahu" ƙafa Uku da nufin Allah ya kai haske zuwa ga Sheikh Adamu Tsoho Jos.
Wannan hoton jagora ne Sayyid Ibraheem Zakzaky tare da iyalan gidan Malam Adamu Tsoho Jos wanda suka ziyarce shi a gidansa dake Abuja, kuma jagora ya musu ta'aziyya.
Inna lillahi Wa Inna Ilaihirraji'un!
Marhum Sheikh Adamu Tsoho Jos Bawan Allah Ne Mai Haƙuri Da Sadaukarwa.
Inna Lillahi Wa Inna Ilaihirraji'un
Duk abin da Allah ya hukunta wa mutane shine dai-dai sai a karɓa hannu bibbiyu, Rasuwar Sheikh Adamu Tsoho ta zama babban jarabawa ga Da'irar Jos da ƴan uwa na Jos, da kuma Ƴan uwa na yankin Jos. A lokaci guda rashin Marhum Sheikh Adamu Tsoho rashi ne wanda aka yiwa Harka Islamiyya baki ɗaya da duk ɗan uwa mabiyin Sayyid Zakzaky (H) dama Musulmi mai son shariya.
Jagora Sayyid Zakzaky (H) ya shaidi Marhum Sheikh Adamu Tsoho da kyakkyawar shaida na mutanen kirki, ya ambata cewa; "Malam Adamu ya bayar da dukkan rayuwarsa a kan yi ma addinin Musulunci hidima ta hanyar karatu da karantarwa, kuma mai gwagwarmaya ne wajen tabbatar addinin"
Sannan ya ƙara yin shaida akan Marhum Sheikh Adamu Tsoho da cewa " mutumin kirki mai kyawawan halaye. Ya kuma bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi. Yace, muna masa fatan alkairi, kuma ya yi karshe mai kyau insha Allah, Ko da wane lokaci za a yi ta tunawa da su, musamman a dararen Juma'a".
Marhum Sheikh Adamu Tsoho Jos ya koma ga Allah ne a ranar Talata 30 Juli 2024 dai-dai da 24 Muharram 1446h. Kafin rasuwar Sheikh Adamu Tsoho ya Kasance wakilin Ƴan uwa Musulmai Almajiran Sayyid Zakzaky (H) na Da'irar Jos, Sheikh ya sadaukar da dukkan rayuwarsa tun yana matashi har tsufansa a gwagwarmaya tabbatar da addinin Allah.
Kuma anyi addu'ar bakwai na rasuwarsa a ranar Talata data gabata 5/08/2024 wanda aka gudanar kamar haka:
Rana: Talata Lokaci: 8:00am na safe
Guri: Gidan Sheikh Adamu Tsoho dake Unguwar Rogo.
Sheikh Adamu Tsoho Jos ya tsayu akan koyarwa da karantarwa, kusan dukkan lokacin rayuwarsa yayi shine wajen bada karatu ga al'umma. Sheikh Adamu Tsoho an shaide shi da kyawawan Dabi'u, hatta Al'umma gari sun masa wannan kyakkyawan shaida, daga cikin wakilan Ulama'u na Jihar Filato a lokacin da suka zo ziyara sun shaidi Marhum Sheikh Adamu Tsoho a matsayin mutum marar Kwaɗayi wanda bai damu da abin Duniya ba.
Rayuwar Sheikh Adamu Tsoho Jos ta zama abin koyi ga duk musulmi, hatta wanda ba Musulmai ba sun zo gidan Sheikh Adamu Tsoho sun kawo ziyara kuma sun yabi kyawawan halaye da ɗabi'u da iya mu'amala na Sheikh Adamu Tsoho. Yau Talata 06 ga watan Agusta 2024 Sheikh Adamu Tsoho ya cika kwanaki Bakwai (7) da barin duniya kuma an gabatar da Addu'oi da Saukar Karatun Alkur'ani mai Girma a ƙofar gidan sa dake Anguwar Rogo Jos.
Wannan rahoton yana dauke hotunan wajen addu'a Bakwai (7) ne na Marhum Sheikh Adamu Tsoho Jos da ya gudana a safiyar yau Talata, wanda aka yi sauƙar Alkur'ani da karanta addu'oi ma'asurai daga Littafin Mafatihul Jina. Allah ya Haskaka makwancin Sheikh Adamu Tsoho yasa Aljannah ta zama makomarsa.
Shima Sheikh Yakubu Yahaya Katsina Yayi Nasiha ga Yaya da yan'uwa na Jos inda yake cewa: Kada Ku Bari Wuta Ta Mutu A Hannunku Ku Cikawa Malam Adamu Alƙawarinsa A Bayan Rayuwarsa.
Wal-aƙibatu Lil Muttaƙin!
Musulunci ya samu giɓi da raunin da ba abin da zai iya toshe wannan giɓin, wannan shine matsayin mutuwar Malam Adamu, akwai abin shaida a Rayuwar wannan bawan Allah wanda muke tare da shi kusan Shekaru 40 muna faɗi tashi a cikin halin tsoro , da halin aminci, da halin Kunci dukka muna tare. Muna tare a lokacin Ribaɗi da muka yi a Jihar Kaduna cikin wani daji da ake cewa "Dajin Jere" kwanakin mu 40 a wannan wajen bamu taba ganin dan adam ba ɗan adam ma bai gammu ba har muka dawo cikin gari.
Banda wannan ma kafin shi ya Halarci wani Ribaɗi tare da su Malam (H) a garin Maiduguri. To, kuma iyakan zama na da su Malam Adamu ban san abokin fadan sa ba, sai dai ayi rigima da shi amma shi baya rigima da kowa. Mutum ne wanda yake mai hakuri mutum ne wanda yake mai ɗaukar girma, Mutum ne wanda ya ke ɗaukar gabata, kuma babu shakka akwai lalurori da ake fama dasu amma idan mutum ya tsaya ya duba nauyin da yake kan Malam Adamu da irin ɗawainiyar da yake wa addini zamu ga cewa har da shi ya ƙara duƙurƙushe jikinsa.
Malam Adamu yana jin nauyin da Al'ummar da ke kansa, Malam Adamu yana iya karatu a mutane akan Maudu'i ɗaya yakan yi zama 61 wani maudu'i 85, duk don a shiryar da al'umma, amma a duba muhallin da Malam Adamu yake zaune da iyalinsa ba nashi bane . To, amma tunda rayuwar haka ta zama sai ya sa hannu ya karba, hakan bai hana shi ya bada gudunmawa ga addini ba, bai hana shi ya jajirce iyakar jajircewa ba. Muzaharori wanda aka shiga aka fita da kyar da shirye-shirye kawarwa duk an shiga an tsallake saboda tawakkalin sa ga Allah da jajircewansa.
To, mu yanzu mune abin tausayi saboda shi yanzu munga yadda ya cika, ya gama bada Sallah Azahar Da La'asar ya dauko carbinsa zai ja, sai Allah Ta'ala ya saukar masa da lalura na ajali wanda aka yi kokari zuwa asibiti kafin aje kuma rai yayi halinsa. Abin da ake nema kuma shine "Kyakkyawar Cikawa" mun yi waya shi kwana ɗaya kafin rasuwar sa nace mishi tunda muka dawo daga Abuja bamu gaisa ba, duk da yake nima kwana ta kusan biyar ban bana jin dadi ina nan kwance, na fito kenan zan je ta'aziyya wani rasuwa da gaisuwar marar lafiya kan hanyar kenan wannan labarin rasuwar ya riskeni.
Naga kuma lallai babu makawa illa in taho nayi ta'aziyya, in mika jajena musamman ga shi Jagora (H) da kuma sauran yan'uwa da iyalansa da al'umma baki ɗaya. Ba rasa shi muka yi ba ya tafi daga gare mu ne in muka kiyaye ayyukansa da Koyarwasa da tarbiyya da ya bamu babu abin da zai salwanta bil hasani ma cigaba da za'a gani, kuma hanƙoronsu kenan su gina mu kuma an gina. Ni dai Nasihar da zan yi gare mu shine kafa mu bari wuta ta mutu a hannun mu, mu da yanzu Allah ya nufe mu da kai da dawowa na shige da fice domin wannan gwagwarmaya idan bamu nan wa muke saka ran zai maye gurbin mu ?
Hankoron mu shine ya zamu yi mu gina masu maye gurbin mu, domin wannan aiki ba na rana ɗaya bane , bana lokaci daya bane, zai ci rayuka ne wannan su zo su wuce wannan ma su zo su wuce har Allah ta'ala yayi ikonsa. Shehu Usman Ɗan Fodiyo bashi ya fara ba kafin shi amma shin ya cimma manufar. Imam Khumaini ba shi ya fara ba kafin shi akwai su wani bawan Allah da ake ce masa Almufatti da wasu manyan malamai sai shi Allah ya nufa yayi nasara kammalawa. Kada muji abin ba ya yiwuwa muna da fata a wurin Allah (T), alƙawarin Allah ne kuma Lallai Allah baya saɓa alƙawari.
Tayar da malam a cikin mu da kuma wannan kira da Malam ya shelanta, to ba wasa bane da gaske ne Allah yana nufin mutane da shiriya su dawo ma addini shi yasan ya Allah ya tayar da su Malam (H) ya kawo shi yayi wannan kira. Don haka muyi godiya ga Allah ta hanyar rike wannan kira ta hannu bibbiyu. Su kuma iyali da ƴaƴa ayi zumunci , don ance a satin nan Sheikh Adamu ya kira ya'yansa gaba ɗaya ya yace su hada kansu wuri guda kada su samu cece kuce a tsakanin su. Shi yasa da suka min tambaya gane da ina za'a kai shi nace a duba maslaha su yayansa ina suke so saboda a cika masa burinsa kuma shine abin da yake so.
Mu yanzu mune abin tausayi, Malam Adamu tasa tayi kyau, ya gama lafiya kuma Alhamdulillah yayi kyakkyawar cikawa. Kamar yadda Manzon Allah (Saww) yake cewa; 'Da Me Mutum Ya Cika ' shi ake la'akari dashi ba yawan ibada ba, yawan ibada sallah azumi da sauransu duk wannan ayyuka ne kyawawa wanda yake nuna mutum yana kusanci ga Allah (T), Amma da me ya cika menene karshen aikin sa shi ake la'akari dashi to kuma shi gashi an masa taufiki da wannan, Ni Nasan burin Malam Adamu shine shahada to muna fatan Allah Ta'ala ya saka shi cikin Shahidai ya cika masa burinsa ya riskar dashi da Imam Hussain (As) da dukkan A'imma baki ɗaya.
Malam Adamu yana kishin yada karantawa Ahlulbait babu albashi babu Alawus babu Garatuti babu Fenso a haka ya rayu da iyalansa kuma yana da bukatu na dukkan mutane a gidansa , amma ya hakura domin ya shirya da al'umma, muna fatan Allah ya karbi ayyukansa. Muna gaban iyayen mu muna ganin su aka wayi gari yanzu babu su yanzu mu ake ganin mun zama Baba haka Allah Ta'ala ya tsara Sunnah sa kenan, wannan su tafi su barwa wannan haka dai ake tayi har Allah ya dauke kowa ya gaje kasar sa saboda haka muna fata wanann ƙokari da Malam ya fara to dan Allah don Annabi kada wuta ta mutu a hannun mu ya zama an cigaba da yin komai.
Mun shaida shi Malam Adamu ya rayu akan Hadafi ya mutu akan Hadafi (Hadafi Muƙaddas) sahihin hadafi na ranar da addinin Musulunci da kuma kira wajen raya addinin Musulunci da kishin addinin Musulunci. Malam Adamu ma'abocin sadar da zumunci ne saboda haka idan muna son mu faranta masa muma mu dage da sadar da zumunci Kada mu yanke , sai ya zama ayyukan da sauransu yana ganin tunda Mamaci yana zuwa ziyara, wasu zasu ganshi a mafarki domin yanzu yana barzahu ne, yana ma'ajiyar inda ake ajiye gangan jiki a kabari ruhi kuma barzahu
Ya tabbata daga cikin abin mutum yake so idan yana kabari shine ƳaƳansa suna masa addu'a, aikin alkhairi da ya gina na karatu kuma al'umma suna ta ji tsawon shekaru da ayyukan da yasa aka yi na alkhairi da kuma biyan bukatun al'ummar Musulmi mabanbanta fahimta, Malam Adamu an san shi baya wariya kowa nashi ke hatta wanda ba Musulmi ba yana ƙoƙarin jawo su jiki mu shaida ne mun gani kwanakin baya nan wata ƙungiya ta zo ta karrama shi kuma galibi su ba musulmai bane saboda kyawawan ayyukansa wannan alama ce ta karban kyawawan aikin sa wajen Allah (T) Yana aiki ma "Insaniyya" domin mutumtaka kuma haka Allah yayi umarni.
Kamar yadda nake faɗa a maƙabarta Muna da maganan ganganu da muka yi da shi wanda ƳaƳansa da matansa basu sani ba, nima haka abin yake yasan nawa wanda babu wanda ya sani, wannan kuma wata hira ce wanda sai a Aljanna za'a ƙare ta. Muna fatan Allah yasa makomar mu aljanna, Allah ka mana Rahama Allah ka jiƙan mu ka tausaya mana.
A madadina da iyalai na da sauran yan uwa da muka baro gida muna da yankin mu Katsina baki ɗaya duka muna miƙa sakon ta'aziyya mu ga iyalan wannan bawan Allah muna fatan Allah ya baku hakuri, haka aka yiwa kowa Ƴaƴa su fahimci wannan. Sannan kuma ƴan uwa su sa shi cikin addu'oi mu musamman su ƳaƳa su sani ana binsu bashin addu'oi daga nan har ku bar duniya, kamar yadda yake wa yiwa mahaifinsa har ya bar Duniya da ayyuka na alkhairi da ziyarori ku zama masu zumunci Kada ku biyewa shaidan ya hana ku yin aikin alkhairi da sadar da zumunci yanke zumunci haramun ne.
Wannan itace ganawar Sheikh Yakubu Yahya Katsina da ƴan uwa na Jos bayan an dawo daga Makabarta wajen Bisne Sheikh Adamu Tsoho Jos a ranar Laraba 31 ga watan Juli 2024 wanda yayi dai-dai da 25 ga watan Muharram 1446h a gidan Marhum Sheikh Adamu Tsoho inda ake zaman makokin rasuwarsa.
04-Aug-2024.
Akwai kuma wasu daga cikin Hotuna na Ƙungiyoyi da Fuskokin Mutane da suka zo Ta'aziyyar Marhum Shaikh Adamu Tsoho Ahmad Jos na cikin Garin Jos da wajen Gari a Jiya Asabar 3/August/2024, a Jiyan mun samu Baƙuncin Ƙungiyoyi irin su Ittihadu Anwarul Hidaya, Ittihadu Shu'ara, Ƙungiyar masu Anguwanni na cikin Garin Jos tareda Ba'adin Mutane Waɗanda baramu iya Ambaton su.
Kuma Alhamdulillah kowanne daga cikin Ƙungiyoyi da Mutane idan suka zo sukan yi Kyakkyawar Shaida gami da nuna Alhini tareda Addu'a ta Musamman ga shi Marhum Shaikh Adamu Tsoho Ahmad, Muna Fata tareda Roƙo Ƴan'uwa zasu Cigaba da yiwa Marhum Addu'o'i na Musamman da Nufin Allah Ta'ala Ya Jaddada Rahama ga Ruhin shi Alfarmar A'immatul Ma'asumin.
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صلي على محمد وال محمد.
أعظَمَ اللهُ اُجورَنا بِمُصابِنا بِالحُسَينِ (عليه السلام) وَجَعَلَنا وَإياكُم مِن الطَّالِبينَ بِثأرِهِ مَعَ وَليِّهِ الإمام المَهديّ مِن آلِ مُحَمَّدٍ (عليهم السلام).






















































































