Kamfanin dillancin labaran shafin
sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya habarta maku cewa: an
gudanar da jana’izar gawar Hajiya Shahida Wasila Alhaj Ahmad Baidoun wacce ta
yi shahada a harin da jiragen yakin yahudawan sahyuniya suka kai a yankunan kudancin
birnin Beirut, babban birnin kasar Labanon. Bayan jana’izarta an binne ta a
garin "Al-Shahabiya" da ke kudancin kasar nan.
