Mashawarcin soji na kungiyar Hizbullah, wanda gwamnatin ta'addancin Isra'ila ta kai hari kansa.
Rahotanni sun bayyana cewa, wanda aka hara a harin da aka kai a Dawahi birnin Beirut Haj Fa'ad Shukari ne wanda da aka fi sani da Al Haj Muhsin.
Haj Muhsin Ya kasance cikin jerin sunayen wadanda gwamnatin sahyoniyawan ta ta'addanci ta ke nema kuma daya daga cikin manyan mashawartan kungiyar Hizbullah.
Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai wani harin jirgin sama mara matuki a Beirut babban birnin kasar Lebanon domin kashe wani babban kwamandan kungiyar Hizbullah a ranar Talata.
Kamfanin Dillancin Labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (AS) - ABNA- ya habarta maku bisa nakaltowa daga kamfanin Dillancin Labarai na Labanon (NNA) inda ya ruwaito cewa an kai harin ne da wani jirgin sama mara matuki wanda ya harba makamai masu linzami guda uku. Ta ce an kai harin ne a yankin da ke kusa da Majalisar Shoura ta Hizbullah a unguwar Haret Hreik a birnin Beirut.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hari kan wani kwamandan kungiyar Hizbullah da gwamnatin ta yi ikirarin cewa shi ne ke da alhakin harin roka da aka kai kan tuddan Golan da ta mamaye a makon jiya.
Hukumar ta ce mayakan Hezbollah na kasar Lebanon ne suka kai harin roka a Golan, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane goma sha biyu. Hizbullah dai ta musanta hannu a cikinta.
Shi ne mafi girman soja a kungiyar Hizbullah kuma mai ba da shawara ga shugaban kungiyar Hasan Nasrallah.
Wakilin gidan talabijin na
Ofishin jakadancin Iran a Labanon yayi Allah wadai da keta iyaka da Isra'ila ke yi kan Beirut.
"Muna yin Allah wadai da kakkausar murya kan harin zaluncin da Isra'ila ta kai a kudancin birnin Beirut, wanda ya yi sanadin mutuwar shahidai da dama," in ji ofishin jakadancin a cikin wata sanarwa da aka fitar a shafinta na X.
Wani jami'in kungiyar Amal na kasar Lebanon ya ce 'yan kasar Lebanon ne ke zaune a ginin da aka kai harin. "Abin da ya faru a yau yana canza ma'auni sosai, saboda hari ne a cikin kuryar muhalli."
Harin na sama dai shi ne na farko da aka kai a wata unguwa da ke birnin Beirut tun a watan Janairu, lokacin da wani hari da jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kashe babban jami'in Hamas Saleh Al-Arouri.
https://ha.abna24.com/story/1475674