20 Yuli 2024 - 19:12
Isra'ila Ta Kai Hari Tashar Jiragen Ruwa Ta Hudaida Yaman + Bidiyo

Al-Mayadeen: Sojojin yahudawan sahyoniya sun kai hari kan birnin Hudaidad da jiragen yakinta na F-35.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: a cikin wannan rahoton bisa nakaltaowa daga tashoshin yada labarai zamu ga irin Girman irin wuta da gobarar da wanna harai ya haifar akan tashar jiragen ruwa da ke birni AlHudaida a Yamen.

Kamar yadda aka ji kuma daga tashar labarai Axios cewa: Isra'ila ta fara kai hare-hare kan kasar Yemen.

A bisa rahotannin farko, wadannan hare-haren sun yi sanadiyar shahada da raunata wasu fararen hula na kasar Yemen.