Kamfanin dillancin labaran shafin
sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: wani
mutum da ba a san ko wanene ba ya jefa gurnetin hannu a kan masu zaman makokin Imam
Husani As a yayin taron Muharramul-Haram karo na 13 a hubbaren Imamzadeh Yahya
da ke lardin Sarpul a arewacin kasar Afganistan.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa wakilin kamfanin dillancin labarai na Abna cewa, sakamakon jefa gurnetin bom din da wani da ba a san ko wane ne ba, wasu mutane 7 daga cikin masu makoki Imam Husaini As sun samu raunuka sama-sama.
Wannan majiyar ta bayyana cewa halin lafiyar wadanda suka jikkata a wannan lamari ba abin damuwa ba ne, inda ta kara da cewa an kai wadanda suka jikkata zuwa asibitin lardin Sarpol domin yi musu magani.
A cewar wata majiya mai cikakken bayani, dakarun Taliban da ke wurin da lamarin ya faru, sun hana mahalarta daukar daukar hoton lamarin.
Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan harin na ta'addanci, kuma jami'an Taliban ba su bayar da wani bayani ba dangane da hakan.
Kafin haka dai kungiyar ta'addanci ta Da'esh ta kai hare-hare kan tarukan addini na ‘yan shi'a a kasar ta Afganistan.