18 Yuli 2024 - 10:08
Muhammad Jabara Daya Daga Cikin Jagororin Kungiyar Jama'atu Islami Ya Yi Shahada + Bidiyo

Muhammad Jabara Daya Daga Cikin Jagororin Kungiyar Jama'atu Islami Ta Kasar Labanon Ya Yi Shahada bayan da yahudawan sahyuniya suka kai wa motarsa hari a yammacin Bekaa na kasar Labanon.

Kamfanin Dillancin Labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (AS) - ABNA- ya habarta maku cewa, Muhammad Jabara ɗaya daga cikin jagororin Kungiyar Jama'atu Islami ta Kasar Labanon ya yi Shahada, wannan rahoton yana dauke da Bidiyon daidai lokacin da aka kai wa Muhammad Jabara daya daga cikin jagororin kungiyar Jama'atu Islamiyya ta kasar Labanon a cikin harin da jiragen yakin gwamnatin sahyoniyawan suka kai a yankin yammacin Bekaa.