15 Yuli 2024 - 07:45
Wasu Da Dama Daga Cikin Jami'an Tsaron Iraki Sun Yi Shahada A Yayin Arangama Da Kungiyar ISIS

A yayin arangama da kungiyar ta'addanci ta Da'esh a lardin Diyala na kasar Iraki, jami'an tsaron kasar da dama sun yi shahada.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: a yayin arangama da kungiyar ta'addanci ta Da'esh a lardin Diyala na kasar Iraki, jami'an tsaron kasar da dama ne sun yi shahada.

Rundunar tsaro a lardin Diyala ta sanar da cewa baya ga shahada da jikkatar sojojin Iraki da dama, an kuma kashe 'yan kungiyar ISIS da dama a wannan rikicin.

Hukumar ta sanar a cikin wata sanarwa cewa bayan wannan rikici, an tsaftace tare da gyara wannan yankin da ake magana akai.

A karshen watan Yuni, mayakan na Iraqi sun kuma kai hari kan hangar da motar ISIS a larduna 2 na Diyala da Kirkuk. An gudanar da wannan farmakin ne a daidai lokacin da ake mataki na bakwai na aikin "Takubban Gaskiya" na jami'an tsaron Iraki.