11 Yuli 2024 - 12:10
Wani Jami'in Tsaron 'Yan Shi'a Ya Yi Shahada A Birnin Karachi Na Kasar Pakistan

An kashe wani babban jami'in hukumar yaki da ta'addanci a wani hari da wasu 'yan ta'adda suka kai a birnin Karachi na kasar Pakistan.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA - ya habarta maku cewa: Sayyid Ali Ridha babban jami'in hukumar yaki da ta'addanci ya yi shahada a jiya a yankin Karimabad na birnin Karachi da ke kudancin kasar Pakistan bayan da wasu da ba a san ko su waye ba suka kai musu hari.

Sayyid Ali Ridha yayin da ya ke tare da abokansa a kusa da gidansa, kwatsam sai wasu ‘yan ta’adda guda biyu mahaya babur sukai kurkusa da su ina da suka fara harbe-harben bindiga inda suka same shi suka shahadantar da shi.

Sun harba harsashi 11 a kan Ali Ridha, harsashi hudu sun same shi kuma ya rasu a nan take.

Yayin da jami’an da abin ya shafa ke gudanar da bincike, babu wani hoton CCTV da ke nuna lamarin.

An anyin rakiyar gawar wannan jami'in tsaro wanda aka fi sani da dan Shi'a a birnin Karachi a Hussainiyyar Shuhada’i Karbala kuma an binne shi a makabartar Wadi Husain.

Shafin yanar gizo na 'yan Shi'a na Pakistan ya rubuta cewa: A jiya Aurangzeb Farooqi shugaban kungiyar Sipah Sahaba Takfiriyya ya yi barazana ga cibiyoyin gwamnati yayin da yake ganawa da manema labarai.

Kisan gillar da aka yi wa wannan jami'in Shi'ar a cikin watan Muharram yana nuna raunin cibiyoyin gwamnati da 'yancin da sakewar hannuwan 'yan ta'adda wajen aikata laifukan ta’addancinsu.

Ba za a iya samar da sulhu da zaman lafiya a kasar ba matukar 'yan ta'adda irin su Aurangzeb Farooqi suna yawo cikin walwalaa wannan kasar.