Kamfanin dillancin
labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Mas’ud
Pezeshkian yana tarin kuru’u da suka kai: 16,384,403 kuri'u Dr. Sa’id Jalili
yana tarin kuru’u da suka kai: 13,538,179.
Adadin kuri'un da aka samu a dukkanin rassa na ciki da wajen kasar nan ya kai miliyan 30 da dubu 530 da 157, wanda kuma yawan kuri'un Dr. Mas’ud Pezeshkian ya kai miliyan 16 da dubu 384 da 403, yayin da Dr. Sa’id Jalili ya samu kuri'u miliyan 13. 538,179.
Wanda ya zamo adadin wadanda suka shiga zaben da jefa kuru’u na yana kasar suka kai: 49.8 bisa dari wanda hakan ke tabbatar da Dr. Mas’ud Pezeshkian shine wanda ya lashe zaben.
Ta haka ne ake ganin tare da daukar Dr. Mas’ud Pezeshkian a matsayin zababben shugaban kasa karo na 14 (bayan aiwatar da sa hannun zartar da shi, zai zamo shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran na tara).
