4 Yuli 2024 - 17:51
Mubahalah Shaidar Hujja Ce Akan Fifikon Imam Ali (As) Ga Kowa Baya Ga Manzon Rahama (SAWA)

Amirul Muminina Ali, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a majalissar shawara ta mutane shida da halifa na biyu Umar ya kafa ya shiryata domin zabar halifa a bayansa, domin tunatar da wadanda suke wurin kan hakkinsa da cancantarsa, ya ambaci batun saukar wannan ayar ta Mubahalah mai girma da kuma yi wa ‘yan majalisar jawabi cewa: Shin akwai wanda ya yi tarayya da ni da wannan falalar? Dukkan ’yan majalisar sun yarda kuma sun yi Tabbatar da cewa wannan ayar ta sauka ne domin girmama Imam Ali (As).

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti (A.S) - Abna - ya kawo maku tsokaci dangane da batun Mubahalah wanda ya zamo lamari ne mai ban mamaki wanda bai gaza Ghadir muhimmanci ba domin Mubahalah ita ce ginshikin Ghadir kuma a gaban Ghadir, Allah Subhanahu Wa Ta'ala ya ambace Amirul Muminina Ali (AS) mai albarka a cikin Alkur'ani mai girma a matsayin ruhin Annabi (SAWA).

Lamarin Mubahala Mai Girma Yana Nuna Fifikon Ahlul Baiti (Amincin Allah Ya Tabbata A Gare Su) Ta Hanyoyi Da Dama.

Hanya ta farko: bisa ga umurnin Allah, gayyatar da Manzon Allah (SAW) ya yi wa Amirul Muminina Ali  da Sayyida Fatima Zahra’a da Imam Hassan Mujtaba da Sayyidush Shuhada Imam Husaini, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, ya nuna cewa lallai ne: wadannan mutane masu daraja su ne mafi soyuwa ga Manzon Allah (SAW) kuma a fili yake cewa mafi soyuwa ga Annabi (SAW) shi ma zai kasance mafi falala da alheri ga al’ummar Annabi (SAW).

Hanya ta biyu: Gayyatar da Manzon Allah (S.A.W) ya yi wa Ahlul Baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, don yakar makiya addini, yana nuna daukaka da darajar matsayi da daukakar su a wajen Allah. Domin Manzon Allah (SAW) ya zabi Amirul Muminin (a.s) ne kawai, da Sayyida Fatima (a.s), da Imam Hasan Mujtaba (a.s), da Imam Husaini (a.s) daga cikin su  matansa da danginsa, wanda mafi cancanta zababbu daga cikin Bani Hashem da danginsa da matansa. A cikin wannan al’amari bai yi tarayya da wadannan ma’abota daraja na daga sauran iysalansa ba, balle ma har ta kai gay a zabi wasu Sahabbai ko sauran musulmi!

Hanya ta uku: Wani bangare na lamarin Mubahala shi ne fifikon Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) da ya zamo taimakon addinin Allah ta hannunsu ya faru.

Yayin da Manzon Allah (SAW) ya fita tare da Ahlul Baitinsa don Mubahala, sai ya ce musu: “Duk lokacin da ni addu’ar tsinuwa, ku ce Amin”. Wannan tsarin shirin yana fayyace karara kan rawar da Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) suka taka wajen tabbatar da annabci da hakikanin maganar manzon Allah (SAW), haka nan yana nuna cewa idan makiya addinin Allah suka shiga mubahala tare da su, Allah ta hanyar Ahlul-baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, zai kaskantar da makiya shariarsa da addininsa tare da halakar da su.

A fili yake cewa wanda yake da irin wannan matsayi a cikin yin Mubahalar Annabawa, Salamullahi Alaihim, to tabbas; Ya fi wadanda ba su da wannan matsayi daraja da daukaka kenan.

Don haka ayar Mubahalah tana nuni da fifikon Amirul Muminin a cikin al'ummah, kuma a bisa ijma'in dukkan musulmi, wanda ya fi falala ya cancanci Imamanci da khalifanci a doron kasa baya ga Manzon Rahama (SAWA) shi ne wanda ya fi kowa falala da fifiko da daukaka acikinsu, kuma wannan lamari ne da hatta masu son zuciyar Ta’assubanci irin su Ibn Taimiyyah suka yarda tare da tabbatar da shi.

Babu shakka babu wanda ya damu da makomar musulmi kamar Annabin Musulunci Muhammad (SAWA). Shi ne wanda wahalar da musulmi ke ciki ke damun sa, kuma yana mai tsananin kwadayin shiryar da su, mai tausayi da jin kai ga muminai.

Don haka dukkan musulmi sun yi imani da cewa a karshen rayuwarsa Manzon Allah (S.A.W) ya bar abubuwa guda biyu masu dawwama kuma masu ‘yantar da al’ummar musulmi daga bata da ba za su taba rabuwa da juna ba wato Liffatin Allah Mai Girma Da Iyalan Gidansa Tsarkaka.

Kowa ya sani cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya san sirrin dawwamar Musulunci da girma da daukakar Musulmi da hanyar samun kubuta daga bata da rarrabuwar kawukansu da rashin tsari a cikin abubuwa guda biyu kawai;

1- Rikonsu da Karkon igiya tabbatacciya, daga sama zuwa kasa, watau “Alkur’ani”.

Na biyu: Mafakar kogon tsira kuma kagara mai karfi ta addini, wato “Ahlul Baiti Amincin Allah ya tabbata a gare su”.

Wannan shi ne yadda girman Mubahallah ke bayyana a fili na girmama Alkur'ani da binsa sau da kafa da girmama Ahlul Baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su da binsu sau da kafa.

To yanzu ya zama wajibi ga duk wani musulmi mai hankali ya girmama wannan rana mai girma da muhimmanci, ko da kuwa karamin mataki ne, wajen daukaka darajar Musulunci da Ahlul Baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Inda zamu mu shaida kuma mu lura da wanzuwar wannan gagarumar nasara tare da bullowa da bayyanar tare da kafa hukumar ma'abociyar ma'anar halitta ta wanda akai alkawarin zuwansa, Shugabanmu Baqiyallahil-A’azam, limamin zamaninmu Allah Madaukakin Sarki Ya gaggauta bayyanarsa ami albarka.

Madogara:

An kawo batun Mubahalah a cikin littafai masu yawa daga littafan Shi'a da Sunna. Wasu daga cikinsu sune kamar haka mai bukata sai ya je ya duba da kansa don ya tabbatarwa da kansa hujja yayiwa kansa zabi akan lamarin duniyarsa da lahirarsa:

1- Liffatafin Bihar Al-Anwar; Juzu'i na 21, shafi na 280-354.

2- Littafin Iqbalil-A’amal; shafi na 310-348.

3- Al-Irishad fi ma’arifatil hujajillahi alal Ibad; Sheikh Mufid, Juzu'i na 1, shafi na 169, Darul Mufid.

4- Al-Kashshaf; Zamakhshari, juzu'i na 1, shafi na 283.

5- Tafsirul-Razi; Fakhrazi, juzu'i na 4, shafi na 240.

6- Sahihu Muslim; Muslim Al-Nishaburi, juzu'i na 12, shafi na 129, H. 4420.

7- Fathul Bari; (Sharh Sahih Al-Bukhari), Ibn Hajar Asqalani, juzu'i na 7, shafi na 74.

8- Ihtijaj Sheikh Tabarsi, juzu'i na 1, shafi na 194.

9- Al-Sawaiqil-Muhriqa, Ahmad bin Hajar Al-Hitami, shafi na 156.

10- Tarikh Madinat Damashq, Ibn Asaker, juzu'i na 42, shafi na 432.