Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti (A.S) - Abna - ya kawo maku
tsokaci dangane da batun Mubahalah wanda ya zamo lamari ne mai ban mamaki wanda
bai gaza Ghadir muhimmanci ba domin Mubahalah ita ce ginshikin Ghadir kuma a
gaban Ghadir, Allah Subhanahu Wa Ta'ala ya ambace Amirul Muminina Ali (AS) mai
albarka a cikin Alkur'ani mai girma a matsayin ruhin Annabi (SAWA).
A cikin wani rubutu da Shekh Murteza Najafi Qudsi ya yi yayin da yake bayani kan mas’alar Mubahalah da ma’auninta da manufofinta, ya dauki wannan lamari a matsayin daya daga cikin muhimman shaidu na ingancin gaskiyar cancantar Ahlul Baiti (AS) tare da jaddada wajabcin tunawa da wannan rana.
Wannan rubutu ya zo kamar haka:
بسم الله الرحمن الرحيم
(فَمَنْ حَاجَّکَ فِیهِ مِنْ بَعْدِ مَا جَاءَکَ مِنَ الْعِلْمِ فَقُلْ تَعَالَوْا نَدْعُ أَبْنَاءَنَا وَأَبْنَاءَکُمْ وَنِسَاءَنَا وَنِسَاءَکُمْ وَأَنْفُسَنَا وَأَنْفُسَکُمْ ثُمَّ نَبْتَهِلْ فَنَجْعَلْ لَعْنَتَ اللَّهِ عَلَى الْکَاذِبِینَ) (سوره آلعمران-آیه ۶۱)
Da sunan Allah, Mai rahama mai jinkai.
(Don haka duk wanda ya yi jayayya da kai akan haka bayan ilimin da ya zo maka, to k ace ku zo mu kira Yayanmu da Yayanku da Matayenmu da Matayenku da Mu da Ku mu hadu mu yi addu’a mu sanya tsinuwar Allah akan wadanda suke makaryata) (Suratul Ali-Imran, aya ta 61).
Wayewar Alfijir ranar 24 ga watan Zul-Hijja, ita ce safiya, Manzon Allah (SAW) yarda da kai da murmushi, ya shiga fagen fama tare da dattawan addinin Kirista domin mubahala... Sun zo domin su yi Mubahala da juna; Wato dukkan bangarorin biyu su yi addu'a, su roki Ubangiji makadaici, akan cewa duk wanda ya akan gaskiya to addu’arsa ta karbu ya samu dacewa akan amsa addu'arsa, wanda kuma ya ke kan bata da kuskure, wanda ya bay a kan gaskiya, ya kasance maqaryaci, ya yazamo ya tozarta, kuma azabar Allah mai girma ta sauko masa.
Babu shakka daya daga cikin fitattun abubuwan da suka faru a tarihin Musulunci, wadanda aka saukar da ayoyi guda tamanin na Suratul Al-Imran, shi ne waki'ar "Mubahalah".
Wani al'amari mai ban mamaki wanda ya kasance mai mahimmanci, wanda idan har bai yi daidai da matsayin "Ghadir" mai daraja ba to bai gaza da matsayin darajar sa ba. Domin kuwa “Mubahalah” ita ce ginshikin “Ghadir” kuma tun kafin gudanar Ghadir, Allah Subhanahu Wa Ta’ala a cikin Alkur’ani ya bayyana karara cewa Amirul Muminin ‘Ali bin Abi Talib Amincin Allah ya tabbata a gare shi’ ya kasance a matsayin “rai” da kai” na Annabi (SAW) Kuma wannan baiwar Allah da falala mai girma an sanyata da kebenceta ga wannan Imamin. “Saboda haka wanda ya yi jayayya da ku a cikin batun cewa (cewa Isa ba dan Allah ba ne) a bayan ilimin da ya zo muku to, ku ce: Ku zo; Mu zo da ’ya’yanmu kuma ku kawo mana ’ya’yanku muma muzo da matanmu, kuma ku zo da matanku, muma mu zo da kanmu, kuma ku zo da kanku. Sannan mu yi Mubahala mu roki tsinuwar Allah ta fada kan Makaryata”. Manzon Allah (SAW) bayan fathu Makkah, a watan Shawwal na shekara ta tara bayan hijira, bisa umarnin Allan Ta’ala ya ba da umarnin shirya jerin wasikun kiran Kiristocin Najrani zuwa Musulunci. Wadanda suka halarci taron da Manzon Allah (SAW) sun kasance manya-manyan malamai ne na Kiristoci wadanda suke tafiyar da gwamnatin addinin Kirista a wancen lokacin.
Bayan karanta wasiƙar, babban bishop ya yanke shawarar yin shawara ne kafin ya tsaida matsayinsa dangane wasikar. Bayan musayar ra'ayi a wajen shawarar, sai suka gudanar da babban taro a babban cocinsu.
Da farko babban limamin ya karanta wasikar Manzon Allah (SAW) ga jama’a domin su bayyana ra’ayinsu. Daya daga cikin manyan malaman addinin Kirista mai suna "Haritha" ya tabo bincike kan gaskiyar Manzon Allah (SAW) yana mai tabbatar masu da cwa Annabi Muhammad (SWA) shine akan gaskiya. Da jin haka sai shi kuma babban Bishop ya ba da umurni cewa a karanta wa mutanen da ke cikin babbar Cocin dukkan nassosi karara da suka zo kai tsaye da suka anbaci Muhammadu da iyalan Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi daga Littafaai masu tsarki da suka hada da: Littafin Adam, Littafin Ibrahim, Littafin Shith, Attaura da Littafi Mai-Tsarki na Linjila.
Ta hanyar karanta litattafai da littattafan annabawan da suka gabata, ya bayyana ga kowa da kowa cewa, bisa ga waɗannan nassosi, Annabi (SAW) ya fito daga zuriyar Ibrahim da Isma'il, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, kuma zuriyarsa daga 'yarsa za su kasance, wanda shi ne na karshen annabawa ana kiransa da "Muhammad" kuma yana da wani sunan wanda shi ne “Ahmad”. Addininsa nag aba dayan duniya ne ba wai ya kebanta da ‘ya’yan Ismail ba. Kuma wannan d yake shi ne mai ceton bil’adama, wanda zai cika duniya da “adalci”, shi ne Da na ƙarshe kuma magaji na goma sha biyu na daga tsatsonsa ne.
Bayan karanta waɗannan nassosi, an yi nasara akan masu shakka da masu ƙaryatawa na daga cikin Kiristoci, amma duk da hakan basu mika wuya ba. Daga nan ne sai suka zo Madina bisa jagorancin babban Bishop nasu domin su ga Annabin karshe (SAW) da kyau da kuma gwada halayensa da maganganunsa da sifofin da suka samu a cikin littattafansu. Amma har kwana uku da zuwansu Manzon Allah (SAW) bai yi magana da su a kan babban al’amarin da suka zo domin shi, kuma suma ba su tattaunawa da Manzon Allah (SAW) akan hakan ba.
A rana ta uku, Manzon Allah (SAW) ya kira su zuwa Musulunci. Amma duk da sun yarda sun tabbatar da halayen Annabi da aka fada acikin littafansu masu Tsarki, sun ƙi karbar addinin musulunci bisa fakewa da cewa Annabi (SAWA) yaki amincewa da Allantakar Annabi Isa As.
Annabi (SAW) ya yi muhawara da su a kan haka. Amma har yanzu sun yi inkarin hakan ba su yarda da hujjojin Annabi (SAWA) ya gabatar masu ba, sai suka bada da shawarar cewa ayi Mubahala. A wannan lokacin ne Allah Madaukakin Sarki Ya aiko da “Ayar Mubahallah” zuwa ga Annabi (SAW). Haka nan Manzon Allah ya karanta musu abin da aka saukar zuwa gare shi ya ce: “Allah Ya umarce ni da cewa idan kuka tabbatu akan kalmanku, zan amsa rokonku, in yi Mubahala da ku”.
Biyu daga cikin Kiristocin Najran, wadanda suka fi kowa sanin gaskiya, kuma suka fi tsoron Mubahala, suka ce wa sahabbansu: “Idan ya zo Mubahala tare da mu tare da sahabbansa da jama’arsa, za mu yi Mubahala tare da shi, domin wannan shi ne dalilin da ke nuna cewa shi ba annabi ba ne.
Amma idan ya zo Mubahala da iyalinsa, ba za mu yi Mubahala tare da shi ba; Domin ba zai jefa iyalinsa cikin hatsari sai dai ya tabbatar da gaskiyarsa. Babban limamin cocin ya amince da wannan magana.
Allah Madaukakin Sarki ya dauki nauyin shirya rundunar Musulunci a gaban sahun rundunar Kiristocin Najran. Don haka ayar Mubahalah umarni ce ga Manzon Allah (SAW) a aikace kuma wajibi ne ya zo “‘ya’yansa” da “Matansa” da shi “kansa” wurin saboda wannan shine umarnin ubangiinsa kamar yadda Ayar ta nuna: « أَبْناءَنا وَ أَبْناءَکُمْ وَ نِساءَنا وَ نِساءَکُمْ وَ أَنْفُسَنا وَ أَنْفُسَکُمْ ».
Da fitowar rana a ranar Talata 24 ga watan Zul-Hijja, shekara ta 9 bayan hijira, a shekara ta 631 miladiyya, Manzon Allah (SAW) ya tafi wurin Mubahalah, yayin da Amirul Muminin Salamullahi Alaihi ya kasance a matsayin “Rai da Kai ” na Manzon Allah (saww) ya tsaya kafada da kafada da shi yana rike da hannun dama na Manzon Allah (SAW) Imam Hasan (a.s) kuma yana bangaren hagu na Manzon Allah (SAW) shi kuma Imam Husaini (a.s) a rungume a hannun Manzon Allah (S.A.W). dukkansu suka kewaye haske na musamman na dukkan halitta majidadin Sarautar Allah Ta’ala Sayyida Fatima Zahra (amincin Allah ya tabbata a gare ta) haka suka taho domin su zama masu amsa Ameen na addu’ar Annabi Muhammad (SAWA) da zata gudana tare da dattawan Kiristoci.
Karamar A’immah (a.s.)
Mutane biyar masu tsarki (amincin Allah ya tabbata a gare su) suna masu tahowa sannu a hankali cikin haske. Duniya ta zamo tana mai kallonsu kamar Allah ya kawo aljannah ne ana kallonta. Mutane biyar ma’abuta mayafi tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, suka isa wurin da aka sanya za’a gudanadar da Mubahalar, suka tsaya karkashin babbar riga. Annabi ya daga hannun damansa zuwa sama. Sai ya bude yatsunsa, a lokacin ne ya ce: " Ya Allah wadannan su ne Ahlul Baitina kuma zababbuna ka nesantar da su daga dukkan mummunan abu kuma ka tsarkake su”.
Ya Allah wannan Ali shine a ma’anar “kai na” Kuma shi ne daidai da Kaina a gare ni. Allah, wannan Fatima ce ita ake nufi da "matana" kuma ita ce mafi daukakar mata a duniya. Allah wadannan su ne Hassan da Hussaini ‘ya’yana biyu kuma jikokina. Ni ina yaƙi da duk wanda ya yi yaƙi da su, kuma ina son duk wanda yake sonsu”.
Tun ba’a kai ga yin Rantsuwar Mubahalar ba, amma alamomin fushin Allah sun fara bayyana kuma azabar tana gab da saukowa. Sai mutane biyu daga cikin shugabannin Nasara suka zo wajen Annabi (SAW) suka ce: Ya Abal Kasim, da wa kake son yin Mubahala da mu? Sai Manzon Allah (SAWA) ya ce: "Ina mai rantsuwa tare da ku da mafifitan mutane a doron kasa kuma mafi soyuwa daga cikinsu ga Allah madaukaki”.
Sai Annabi (SAW) ya yi nuni ga Ali da Fatima da Hasan da Husaini (amincin Allah ya tabbata a gare su) ya ce: “da wadannan”. Sannan ya sake nanata masu da cewa: "Shin, ban sanar da ku hakan ba a dan lokaci kaɗan da suka wuce ba?" Na rantse da wanda ya aiko ni da gaskiya, an umarce ni da in yi MUbahala da ku tare da su. Waɗannan su ne 'ya'yanmu da matanmu da kawukanmu. Don haka bisa umarnin babban Bishop na Najraniyawa suka yanke shawara janayewa da barin yin Mubahalar, su ka karbi tare da yarda da biyan haraji (jizya) a tsakaninsu...
Lokacin da Manzon Allah (SAW) da Ahlul Baiti (A.S) suka isa masallaci tare da mutanen wurin Mubahalar, sai Jibrilu ya sauko ya gabatar da wannan sako daga sama: “Ya Muhammadu Ubangiji Ta’ala yana gaishe ka, yana cewa mai cewa:... Ya Ahmad, na rantse da girmana da daukakata, da za kai Mubahala da iyalinka da ke karkashin mayafin, tare da dukkan al’ummar halittu da ke sama da kasa, da sai sama ta wargaje da duwãtsu sun gutsuttsura, kuma ƙasa ta tsage, kuma bã zã ta tsaya tai daidai ba, sai in na so hakan”.
Da jin wannan sako na Ubangiji, sai Manzon Allah (SAW) ya yi sujjada ya shafa fuskarsa a kasa. Sannan ya daga hannayensa ya ce sau uku: "Na gode wa Allah wanda yake yin ni'ima." Sannan ya ce: "La'anar Allah ta har abada har zuwa ranar sakamako ta tabbata a kan wadanda suke zaluntar ku Ahlul Baiti, kuma sukai kas agwiwa suka kasa sauki ladan hakkina da Allah Ya wajabta musu”.
Ranar Mubahalah mai albarka, kafin kowane abu ta raya Annabci da Wilaya, ita ce mafi daukaka da ban mamaki na bayyanar da tabbatacciyar gaskiyar Musulunci madawwamiya, wato "Annabta da cikar Annabci" da "Wilaya da Imamancin Alawi".
A ranar Mubahalah kuwa, an tabbatar da gaskiyar Musulunci a kan sauran addinai da akidoji na tarihi, a daya bangaren kuma ta tabbatar da nuna Ma'aikatan jagoranci na wannan imani na ɗan adam har zuwa ƙarshen zamani.
Ayar Mubahallah ita ce mafi kyawun shaida a kan halaccin Imamanci da halifancin Ali bayan shahadar Manzon Allah (S.A.W), kuma ita ce mafi bayyanan hujjar falalar Amirul Muminin “Ali Bin Abi Talib (As). Domin Allah ya umarci Annabi da ya kirawo kansa zuwa Mubahalah. A fili yake cewa abin da ake nufi da Kan Annabi (SAW) wani mutum ne ba shi kansa ba, kuma shi ne Ali, As a cikin dukkan falaloli da kamaloli, ban da Annabci, darajan da Annabi yake da yana daidai da shi.
Imami na 8, Sayyidina Imam Riza (a.s) ya dauki ayar Mubahala a matsayin mafifici kuma mafi bayyanan aya a cikin Alkur'ani ta fuskar nuna imamancin Amirul Muminin (a.s) kuma bisa dogaro a wannan aya da abin da Manzon Allah (SAW) ya aikata bayan saukar ta, ya tabbatar da cewa Imam Ali Amirul Muminin, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi’ shi ne “Ran Annabi” kuma shine “mafi daukakar halittar Allah” bayan Annabi (SAW).