Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) - Abna – ya kawo maku rahoton cewa: Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen kaddamar da karamin jirgin ruwan kai harinta mai taken "Tufanul-Madammar" (Ambaliya Mai Barna) a ranar Lahadi.
A cewar Tashar Al-Masirah, sojojin ruwan Ansarullah sun sanar da cewa an kera wannan jirgin a cikin kasar ta Yamen.
Shi dai wannan karamin jirgi yana da karfin barna mai yawa kuma yana dauke da kangon yaki mai nauyin kilogiram 1,000 zuwa 1,500.
Ansarullah ta sanar da cewa, wannan jirgin yana da fasahar zamani da manhaja da na'ura mai sarrafa kansa, kuma gudunsa yana kai mil 45 a cikin sa'a guda kuma yana yin aikinsa a dukkan yanayin teku.
Ansarullah ta kuma wallafa wani faifan bidiyo na harin da ta kaiwa wani jirgin ruwa a tekun Bahar Rum tana mai anfani da wannan jirgin nata data Kera a makon jiya.
