1 Yuli 2024 - 05:15
Mubahalah Alama Ce Ta Samun Nutsuwa Da Ikon Imani/ Rawar Da Ahlul Baiti (A.S) Suka Taka Wajen Tsallake Mubahlah Zuwa Yin Sulhu. + Bidiyo

“Ya kamata a girmama Mubahalah kuma hakan yana da matukar muhimmanci, a hakikanin gaskiya wannan lamari ne da ke nuni da kwarjini da karfin imani da dogaro da gaskiya, kuma wannan shi ne abin da a ko da yaushe muke bukata. Dole ne mu dogara da hakan ta fuskar kiyayyar makiyanmu da yin gaba da girman kai, kuma alhamdulillahi muna yi".

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (a.s) bias munasabar ranar Mubahala ya kawo maku takaitaccen bayani dangane da wannan rana da cewa: ranar 24 ga watan Zul-Hijja ta yi daidai da waki'ar Mubahlah, wanda ake ganin tana daya daga cikin muhimman al'amura a tarihin Musulunci, kuma takardar shedar zinare da ke tabbatar da ingancin addinin gaskiya da kuma tabbatar da muhimmin matsayi na Ahlul Baiti (a.s.).

Ana iya kallon Mubahlah a matsayin tarihin kiristoci wadanda suka dauki gurbatattun akidarsu a matsayin tabbatacciyar ingantacciyar akida inda kuma suka tsaya tsayin daka don yin jayayya da Manzon Allah (SAW), amma ba su da karfin fuskantar ilimi da tunani na manzon Allah’ wanda a kowane lokaci suna ganin kansu a matsayin masu asara a wannan yakin. Amma a daya bangaren kuma labarin Mubahlah ya zama mafarin sabon babi a tarihin Musulunci kuma ya gabatarwa da kowa a kan hakikanin matsayin Ahlul-Baiti (AS). Manzon Allah (SAW) ta hanyar tafiya tare da masoyansa zuri’arsa ya isar da sako madaidaici ga kowa da kowa kuma ya gabatar da “Rai da ruhinsa” ga koiwa da kowa, Kuma a sakamakon haka ne Kiristocin Najran suka ja da baya daga Mubahlah, suka amince da yin sulhu.

Imam Husaini (a.s.) wanda ya shaida faruwar lamarin, daga baya ya gabatar da Mubahalah a aikace a Karbala kuma ya kawo fitattun ‘yan uwansa filin domin su fadi tare da bayyana hakikanin gaskiya. Kamar yadda lafazin Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: “Lokacin da makiya suke gurbata yanayi da lalata shi, to ya zama dole a bayar da haske ta hanyar yin Magana ko a aikace; Imam Husaini (a.s) ya aikata hakan, ta hanyar irin wannan sadaukarwa mai nauyi”.

Mubahala, Yin Gaba Da Gaba Ne Tsakanin Fagen Gaskiya Da Karya.

Dangane da haka ne Ayatullah Khamenei a tarurruka daban-daban ya tattauna kan muhimmancin sakon Mubahlah tare da bayyana ma'anoninsa yana mai cewa:

Ranar Mubahlah ita ce ranar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ya fito da mafi soyuwar ginshikai na mutane zuwa ga fage. Muhimmin batu game da Mubahlah shi ne kalmar: «و انفسنا و انفسکم و نساءنا و نساءکم» "Da Kawukanmu Da Kawukanku Da Matayenmu Da Matayenku"; Manzon Allah (SAW) ne ya zabo mafi soyuwar mutane ya zo da su a fage domin a yi muhawarar da ya kamata a bayyana banbanci tsakanin gaskiya da karya da tantancewa mabayyaniya ga kowa. Ba a taba samun wani misali a tafarkin isar da sakon addini da fadin gaskiya inda Annabi ya kama hannun masoyansa, ‘ya’yansa da ‘yarsa da Amirul Muminina – wanda shi ne dan’uwansa kuma magajinsa – ya kai su zuwa tsakiyar fili a cikin fage. Keɓaɓɓen ranar Mubahala ya kasance a wannan yanayi ne. Wato yana nuna muhimmancin fadin gaskiya, isar da gaskiya; Yana zuwa filin da wannan ikirari yana cewa, "ku zo muyi mubahala" Kowannenmu da yake na kan gaskiya ya wanzu, kowannemu da ya sabawa gaskiya, a shafe shi da azabar Ubangiji.

Yayin da akwai mata da yawa a wajen Annabi, su matan Annabi ne, sauran makusantan Annabi, watakila wasu daga cikin ‘ya’yan Manzon Allah (suma) sun kasance a lokacin; Amma “Nisaana -matayanmu” ita ce Fatima Zahra, tsira da amincin Allah su tabbata a gare ta kawai; saboda me hakan ya kasance? Domin fuskantar bangaren gaskiya da bangaren qarya. Fatima Zahra ita ce siffar alama ta wadannan gaskiyiyo masu daraja da ban mamaki. Wadannan su ne kyawawan falaloli na Sayyida Zahra (AS).

Mubahlah, wacce ya kamata a rika tunawa da ita, kuma tana da matukar muhimmanci, hakika ita ce bayyanar tabbatuwa da ikon imani da dogaro da gaskiya, kuma wannan shi ne abin da a ko da yaushe muke bukata. Ko a yau, muna bukatar iko iri ɗaya na bangaskiya da kuma dogaro iri ɗaya ga tamu gaskiyar; Domin muna tafiya a kan tafarki madaidaici, wajibi ne mu dogara da hakan wajen fuskantar kiyayyar makiyanmu da kiyayyar ma'abota girman kai, alhamdulillah kuma muna yi hakan.