Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti
(A.S) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa, Kungiyar gwagwarmaya ta kasar Labanon ta
fitar da wani faifan bidiyo a safiyar ranar Lahadin mai taken "Ga duk
wanda Abun Ya Shafa" da kuma mayar da martani ga barazanar gwamnatin
mamaya ta Isra'ila, Sayyid Hasan Nasrallah, Sakatare. Janar na kungiyar
Hizbullah ta kasar Labanon, ya ce: Idan aka dora mana yaki, to makiya za su yi nadama.
A cikin wannan faifan bidiyo, kungiyar Hizbullah ta nuna kebantattun wurare da cibiyoyi masu muhimmanci nay an mamaya; Tare da nuna cewa a yayin da aka fada mai girma, dukkanin wadannan yankuna suna cikin tsaka mai wuya.
Ginin ma'aikatar yakin Isra'ila a Tel Aviv, matatar mai na Haifa da mahimman wurarenta, filin jirgin sama na Ben Gurion, tashar Ashdod, tashar Haifa, sansanonin soji na tauraron dan adam a yankin Yahud, da sansanonin soji a hamadar Negev da yankin Galili yankuna ne da aka nuna yanayin da suke a cikin wannan bidiyon.
A farkon wannan bidiyo an ambaci wani bangare na jawabin Sayyid Hasan Nasrallah na baya-bayan nan yana cewa: “A cikin yakin da da ya zamo ya tabo ko ina, ba za a samu rufin iyaka ba, babu wata iyaka, kuma babu ka’idoji da dokoki, za a halasta komai da komai kuma komai zai kasance karkashin wutar Hizbullah”.
