24 Yuni 2024 - 13:46
Daga Cikin Hujjojin Imamanci Da Khalifancin Amirul Muminina, Sayyidina Ali (AS) Bayan Manzon Rahama (SAWA) Akwai Ayah Wilayah

Tabbas Lallai majibincinku Abin sani kawai, shi ne Allah da Manzonsa da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suke tsayar da salla, kuma suka bãyar da sadaka, alhãli kuwa sunã mãsu ruku'i. Wanda duk ya jibintawa Allah da manzon da wadanda su kai Imani da Allah lamarinsa to tabbas rundunar Allah sune masu yin rinjaye} (Maedeh/55)

Allamah Amini ya kawo dalilin saukar ayar Wilaya wacce ta sauka game da Sayyidina Ali (AS) a cikin Littafinsa na Ghadir ruwayoyi daga ingantattun littafan Sunna kusan ashirin, tare da ambaton hujjojinta da madogararta.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) -ABNA- ya kawo maku bayani dangane da Ranar Ghadir ranar da Manzon Rahama (SAWA) ya nada Imam Ali As nadi na karshe domin sauke nauyinsa a mataki na karshe na sakon Annabcinsa ga al’umma daAllah ya aiko shi domin ya shiryatar da su.

                Ghadir wani bangare ne mai muhimmanci a tarihin musulunci, wanda wasu ‘yan fashin gaskiya suka rufe tare da karkatar da tafarkin ayari na mabiya musulunci. Wasu mutane suna sane suka da zabin da Manzon Allah (SAW) yayiwa al’ummarsa amma suka nemi mulki da shugabancin al’umma suka bisa zalunci da tsanantawa da takurawa ga iyalan gidan Manzon Allah (SAW).

Dangane da haka ne za mu yi kokarin tabbatar da Imamancin Sayyidina Ali (a.s) dakuma khalifancinsa bayan wafatin Manzon Allah (s.a.w.) a cikin ayoyi da ruwayoyin hadi da riwayoyin tarihi domin fitarwa tare da bayyanar da wannan gaskiyar da aka boye akai inkarinta daga tarihin Musulunci.

Daya daga cikin ayoyin da aka kafa hujja a kan haka, ita ce ayar Wilaya, wacce ta sanya Wilayar Amirul Muminin (AS) Wilayar Allah da Manzon Allah (SAW).

Aya Wilaya:

[ ِنَّمَا وَلِيُّكُمُ اللَّهُ وَرَسُولُهُ وَالَّذِينَ آمَنُواْ الَّذِينَ يُقِيمُونَ الصَّلاَةَ وَيُؤْتُونَ الزَّكَاةَ وَهُمْ رَاكِعُونَ (55) وَمَن يَتَوَلَّ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَالَّذِينَ آمَنُواْ فَإِنَّ حِزْبَ اللَّهِ هُمُ الْغَالِبُونَ] المائدة 55.

Tabbas Lallai majibincinku Abin sani kawai, shi ne Allah da Manzonsa da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suke tsayar da salla, kuma suka bãyar da sadaka, alhãli kuwa sunã mãsu ruku'i. Wanda duk ya jibintawa Allah da manzon da wadanda su kai Imani da Allah lamarinsa to tabbas rundunar Allah sune masu yin rinjaye} (Maedeh/55)

Malaman Tafsiri da malaman hadisi da dama sun ce wannan ayar ta sauka ne dangane da Ali (AS).

Ibn Abbas kawo hakan yana mai cewa: “Ali (a.s) yana a halin ruku’u a cikin sallah sai wani mabukaci ya nemi taimako sai ya ba shi zobensa sadaka, sai Annabi (SAW) ya tambayi mabukacin: Wane ne ya ba ka wannan zoben sadaka? Sai mabukacin ya yi nuni zuwa ga Sayyidina Ali (a.s) ya ce: “Wannan mutumin da yake ruku’u”. A wannan lokacin ne wannan ayar ta sauka.

Malaman Sunna irin su “Siyuti” da “Wahidi” da “Zamakhshari” ne suka ruwaito wannan ruwayar.

Fakhr Razi ya ruwaito daga Abdullahi bin Salam cewa:

Lokacin da wannan ayar ta sauka sai na ce wa Manzon Allah (SAW): Da idona na ga Ali (As) ya ba da zobensa yayin da ya ke ruku’i ga mabukacin. Saboda hakane ma ya sa muka yarda da Wilayarsa!

Tabari kuma ya ruwaito hadisai da dama cewa wannan ayar ta sauka ne akan Sayyidina Ali (AS).

Allamah Amini ya ruwaito saukar wannan ayar game da Sayyidina Ali a cikin littafin Al-Ghadir da ruwayoyi kusan ashirin ingantattu na Ahlus Sunna, tare da ambaton hujjojinta dalla-dalla.