23 Yuni 2024 - 19:00
Ayatullah Ramazani: Halartar Dimbin Al'ummar Iran A Zaben Ranar 8 Ga Watan Tir

Shahid Raisi bai san gajiya ba a hanyar hidima. Shahidan hidima su suka sanya ya zamo za mu shaidi yadda halartar dinbin al’umma a wajen zaben ranar 8 ga watan Tir

A wani bangare na jawabin nasa, Ayatullah Ramazani, yayin da yake ishara da zaben shugaban kasa da kuma girmama shahidai, ya ce: Sun share mana hanyar zabe. Wadannan shahidai masu daraja a fagen hidima sun haifar da amana tsakanin al'umma da jami'ai, kuma duk wanda aka zaba a matsayin shugaban kasa ya zama dole ya ba da fifiko wajen ci gaban hidima da kasancewa a fage. Shahid Raisi bai san gajiya ba a hanyar hidima.

Ya kara da cewa: Shahidan hidima su suka sanya ya zamo za mu shaidi yadda halartar dinbin al’umma a wajen zaben ranar 8 ga watan Tir. Ina da tabbacin cewa a wannan lokaci na zaben shugaban kasa, za a sauke hakkin kashi 40% na zaben da ya gabata. Idan har yanayin tsaro na tsarin Jamhuriyar Musulunci yana son karuwa a duniya, muna bukatar mafi girman halartar mutane.

Babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-baiti (AS) ya bayyana cewa: Yana da matukar muhimmanci a gare mu cewa muga an zabi shugaban kasa da kuri'a mai girman yawa ta yadda zai iya magance matsaloli a fagage daban-daban da kuma tsare-tsaren da suka dace a kan haka.

A wani bangare na wannan taron, mambobin kungiyar "Shahid Arman Media Headquarters" sun bayyana ra'ayoyinsu da shawarwarinsu game da isar da sako a shafukan intanet da kuma fagen kasa da kasa.

...................................