23 Yuni 2024 - 08:15
Ayatullah Riza Ramazani: Yadda Imam Hadi A's Yayi Bayanin Koyarwar Ahlul Baiti (AS) A Cikin Ziyarar Jami’ah Kabirah.

Cikakken Rahoton Taro Mai Taken "Bunkasasshen Zaɓe; Karfin Da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Take Da Shi A Fagen Kasa Da Kasa" Ayatullah Ramazani: Shigar Kowa Da Kowa Cikin Fitar Da Makoma Daya Ne Daga Cikin Koyarwar Ghadir + Hotuna Da Bidiyo.

An Gudanar Da Taron " Bunkasasshen Zaɓe; "Karfin Da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Take Da Shi A Fagen Kasa Da Kasa" tare da jawabin babban sakataren majalisar Ahlul-Bait (AS) ta duniya A birnin Qum.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlal-Bait (AS) -ABNA- ya bayar da rahoton cewa: an gudanar da taron mai taken: " Bunkasasshen Zaɓe Da Karfin Da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Take Da Shi A Fagen Kasa Da Kasa A ranar Asabar 1 ga watan Tir shekara ta 1403 a zauren majalisar Ahlul-baiti (AS) ta duniya a ginin majalisar da ke birnin Qum.

Ayatullah Riza Ramazani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Bait (AS) ne ya gabatar da jawabi a wannan taro, wanda ya samu halartar gungun 'yan kungiyar "Shahid Arman Media Center".

Bayanin Koyarwar Ahlul Baiti (AS) A Cikin Ziyarar Jami’ah Kabirah.

A farkon wannan taro, yayin da yake taya murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Hadi (a.s), Ayatullah Ramezani ya bayyana cewa: Ziyarar Jami’ah Kabirah mai girma ita baun da abun da Imam Hadi (a.s.) ya bar mana da muke tuna shi da ita, wannan ziyarar ta bayyana koyarwa da kuma matsayin shari'a da hakika na Ahlul Baiti (a.s.). Ziyarar Jami’ah Kabirah tana magana ne akan yadda zamu san Ahlul Baiti, kuma ana iya yin bayanin jigogin koyarwar wannan Ziyarah ta hanyar hankali, wato ana iya bayanin jigogin Ziyarar Jami’ah a mahangar hankali da yanayi halitta.

Ya ci gaba da cewa: Wasu ma’abuta ilimi saboda ba su da cikakkiyar masaniya kan koyarwar Ahlul-Baiti (AS) sun yi iƙirarin cewa Ziyarar Jami’ah Kabira ta samo asali ne daga koyarwar Gulat, alhali kuwa duk abin da batutuwan wannan ziyara ta ginu akai ana iya bayyana su a hankalce da a tushen riwayoyi. Fiye da shekaru talatin ina bayani da sharhin Jamia Kabira, kuma ya zuwa yanzu an buga mujalladi uku na wannan sharhin.

Babban sakataren Majalisar Ahlul Baiti (AS) ya kara da cewa: Wani abin tunawa da Imam Hadi (AS) ya bar mana bayan ziyarar Jamia Kabira ita ce Ziyarar Ghadiriya kuma wannan Ziyarar tana daga cikin ingantattun litattafai. Kimanin sifofi da halaye 150 na Imam Amirul Muminin (AS) aka ambace su a cikin Ziyarar Ghadiriya, kuma da wuya bamu da ziyara da magana kan hakikanin Ghadir kamar wannan ziyarar...

Akwai Ci Gaba