22 Yuni 2024 - 10:54
Ansarullah Sun Nuna Jirgin Ruwansu Da Suke Aki Hari Da Shi Ga Jiragen Ruwan Amurka Da Yahudawa + Bidiyo

A Karon Farko Kungiyar Ansarullah Ta Kasar Yemen Ta Nuna Karamin Jirgin Ruwan Mai Suna Tofan-1 Wanda Take Kai Farmaki Da Shi A Tekun Baharul Ahmar.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlal-Bait (AS) -ABNA- ya habarta cewa: Ansarullah, a karon farko jirgin ruwan mai nau'in "Tofan-1 da ta ke anfani da shi wajen kai hari da farmaki ga jiragen ruwan Amurka Da Isra’ila.

 Wannan jirgin ruwan mai linkaya yana da rufin hular yaki mai nauyin kilogiram 150 kuma ya bambanta da saurin gudunsa da kuma ikon yin motsi da gaggawa wajen gujewa radar.

Rahoton na Ansarullah ya bayyana cewa, gudun wannan Shahpad ya kai kilomita 35 a cikin sa'a guda kuma ana amfani da shi wajen kai hari kan tabbatattun abubwa da da masu motsi na kusa da wuraren da ke teku.

Kungiyar Ansarullah ta sanar da cewa a makon da ya gabata ta hanyar anfani wasu jiragen ruwa biyu na yaki sun kai farmaki kan jirgin Tutor a tekun Bahar Maliya, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa tashar jiragen ruwa na gwamnatin sahyoniyawan, lamarin da ya kai ga halaka da nutsewar jirgin.

A ci gaba da goyon bayan al'ummar Palasdinu, kungiyar Ansarullah ta Yaman tana kai hare-hare kan jiragen ruwa na Isra'ila, Amurka da Birtaniya da kuma jiragen ruwa da ke zuwa tashar jiragen ruwa na Palasdinawa da Isra’ila ta mamaye.

Idan dai ba a manta ba a baya-bayan nan ne Amurka da Birtaniya suka kai hare-hare ta sama a wasu lardunan kasar Yemen da suka hada da Sana'a, Hudeidah, Hajjah, Sa'ada, Ta'iz, da Dhamar.