Wannan rubutu wani sashe na fassarar hudubar sallar Juma'a na wannan mako a Alishahr, ranar 14 Zulhijja 1445, 1 ga Tir, 1403, wanda liman Shekh Hujjatul-Islam WalMuslimin Hamidinejad, limamin Juma’ar Alishahr da ke birnin Bushehr.
Muna cikin kwanuka na Imamanci da wilaya ta jajibirin Eid aGhadir Khum, tare da taya dukkan ku murna, dangane da tabbatar da Imamancin Amirul Muminin, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a bayan Manzon Allah (SAW). Ina so in yi bayanin wasu muhimman batutuwa.
Domin tabbatar da cewa bayan wafatin Manzon Allah (S.A.W) dole ne duk musulmi su yi gaggawar amincewa da Ali (AS) a matsayin Imami wamsa kuma yi masa biyayya ya wajaba akan kowa, babu bukatar a koma ga hadisai, kawai ta hanyar komawa zuwa ga Alkur'ani mai girma shima daga cikin ayoyin da suka tabbatar da wannan lamari karara, ya wadatar da mu, zan yi nuni da wasu ayoyin da suka fi shahara a ayoyin Alkur'ani.
1 --- A cikin suratu Ma'ida aya ta 55 tana cewa majibincinku wanda biyayyarsa ta wajaba a kanku shine Allah, sannan kuma annabinsa, sannan kuma wadanda suka yi imani kuma suka bayar da zakka alhalin suna ruku'u, manyan malaman sunna duk sun kasance sun ce wannan ayar ta sauka ne akan Ali (a.s) shi ya bai wa mai tambaya (roko) zobensa yana sallah yayinda yake ruku'u, kuma ta sauka ne game wannan shugaban ne, kuma dangane da cewa idan wannan ayar mai daraja ta kasance game da Ali ce me ya sa akai amfani da kalmar jam'i aka ce wadanda ba a ce wanda ba, ta za mu ce akwai misalai da yawa a cikin Alkur'ani inda ake amfani da kalmar jam'i ga mutum daya, a cikin dukkan malaman Sunna babu ko mutum daya da ya ce ana nufin wanin Ali (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ne.
2 --- Wata ayar kuma ita ce aya ta 67 a cikin suratul Ma'idah, wadda take umurtar Annabi da ya isarwa da mutane abin da aka saukar zuwa gare shi daga Allah, kuma cewa in dai baka isar da abunda aka saukar gareka ba kamar baka isar da dukkan sakon da aiko ba ne kuma ka sani cewa Allah zai kare ka daga cutarwar da kuke jin tsoro daga jama'a. Itama wannan Ayar malaman Ahlus-Sunnah sun ce ta sauka ne a ranar Ghadir, daga nan ne Annabi (SAW) ya gabatar da Ali (AS) a matsayin magajinsa. Taun daga nan zamu san cewa abun da aka umarce shi da ya isar abu ne da mutane zasu nuna martaninsu akai kuma hadari ne tun da Allah ya e zamu zan karrka daga Mutane yadda ba za su iya cutar da shi ba kuma wannan lamari ba zai zama wani abu ba face Imamanci da shugabancin al'umma.
3 --- Wata ayar kuma da tai magana akan Khalifancin Imam Ali As ita ce aya ta uku a cikin suratul Ma'ida, wadda ke cewa a yau kafirai sun yanke kauna daga iya ruguza addininku, don haka kada ku ji tsoronsu kuji tsorona, a yau na cika maku addininku kuma cika maku ni'imata kuma na yarde maku musulunci a matsayin addini sanannen abu kenan wani abu ya faru da har ya zamo cewa kafirai ba za su iya ruguza Musulunci ba kuma wannan abun ba zai zama wani abu ba face an gabatar da shugaban Musulunci bayan Manzo. Allah Sallallahu Alaihi Wa'alihi Wasallama wanda shi ne Imam kuma zai kare Musulunci daga hannun kafirai kuma addinin Musulunci ya zama cikakke tare da Imamanci kuma mafi girman falalar Niima itace samuwar Imam kuma itace Ni'imar abin da Allah Ya ba wa mutane.
4 --- Wata aya ta 59 a cikin suratun Nisa'i da take cewa "Ku yi da'a ga Allah, kuma ku yi da'a ga Annabi da ma'abucin lamari daga cikinku, ko shakka babu ma'abucin umarni ba zai zama wani ba face Imami ma'asumi, saboda idan shugaba mai bada umarni ba ma'asumi ba ne, a wuraren da ya yi kuskure, dole ne a yi masa biyayya kenan, idan ya yi umurni da aikata zunubi, wato wajibi da umarnin Allah kar muyi zunubi kuma dole ne mu yi biyayya tun farko akan umarninsa kaga idan shugaba yayi umarni da yin sabo kuma muka aikata kafa amsamu cin karo kenan, kaga tana yaya zai zamu yin biyayya ga shugaba ta zamo yin biyayya ce ga Allah sai dai kawai idan Shugaban ya kasance Ma'asumi ne hakan zai faru.
Yanzu abin tambaya a nan shi ne, duk da wadannan ayoyi da suke tabbatar da Imamancin Ali, me ya sa mafi yawan musulmi ba su yarda da Imamancinsa ba? Amsa anan shine mafi yawan musulmai suna ganin ma'anar Wilaya shine soyayya da koyi acikin kwawawan halaye da mu'amaloli ba shugabanci da mulki ba, don haka dukkan musulmi suna qaunar Ali (a.s) kuma suna bin shi a xabi’u da muamalarsa, amma ba su yarda da shi a matsayin limami shugaba majibincin lamari su ba kuma magajin Manzon Allah kaitsaye bayan wafatin Annabi Sallallahu Alaihi Wa'alihi Wasallama ba.
--- A yayin da muke sake kara taya murnar Idin Ghadir Khum, ya kamata mu sani cewa Ghadir bai kebanta ga Shi'a ba, sai dai ya zamo abin koyi ne na gwamnatin Musulunci da ke sanya farin ciki ga dukkan musulmi kuma ya zamo shugaban da zai mulke su ya zamo kamar Annabi ne mai tausayi ga masu ilimi da tsoron Allah, kuma mai kula da matsalolin mutane da wahalhalun da suke ciki da bai san dare da rana wajen magance matsalolin mutane.











