Wasu daga cikin malaman Sunnah da suke da babbna matsayin koli a ilimi sun dauki Hadisin Ghadir a matsayin mutawatiri. Hadisin mutawatar hadisi ne da babu shakka ko matsala akansa cewa daga ma'asumi aka same shi:
Babban Malamin Sunnah Shamsuddin Zaahabi Shafi'i (ya rasu a shekara ta 768 bayan hijira) a littafinsa mai suna Talkisul Mustadrak, ya ambaci hanyoyin riwayoyin da aka riwaici hadisan Ghadeer daban-daban kuma yana ganin da yawa daga cikinsu ingantattu ya ce: "Hadisin farko na shi ne: من کنت مولاه فعلى مولاه فهذا علي مولاه اللهم والي من والى mutawatar ne, kuma na tabbata daga Annabi ne aka ruwaito shi”. kuma jumlar “اللَّهُمَّ وَالِ مَنْ وَالَاهُ” ita ma isnadinta mai karfi. Shekh Alusi da Ibn Kathir ma sun nakalto wannan maganar ta sa.
Sannan shima Babban Malamin Sunnah Shamsuddin Jazri Shafi'i (ya rasu a shekara ta 833 bayan hijira) ya ruwaito hadisin Ghadir ta hanyoyin riwaya tamanin kuma ya rubuta littafin Asnal-Mutalib game da wannan batu ya ce: An ruwaito wannan hadisi mutawatiri daga Annabi da Amirul Muminin (Sa).
Hadisin Mutawatiri hadisi shi ne hadisin da wasu gungu mutane suka riwaito daga wasu gungun, wadanda ake kyautata zaton tabbas su din ba zasu hadu akan yin qarya ba a cikin kowane nau’i na matakin isnadi, kuma hakan ya tabbata tun daga farkon isnadinsa har zuwa qarshensa. kuma dogaronsu ya kasance a kan ji ne daga wani ko ji tare da ganin da ido, ma’ana sun isar mana da hadisin da suka ji ko suka gani da idanun ko suka ji da kuinnuwansu ba wani abu ne da ya ginu a kan hankali da ra’ayinsu ba.
Hadisin Mutawatiri yana amfanarwa wajen samun ilimi tabbatacce, kuma ba za a yi watsi da shi ba ko kuma a yi inkarinsa ba tare da yin bincike akan maruwaitansa ba, kuma ba a la’akari da shi a wani adadi na musamman da yawa ko kadan wajen gane matsayin mafi ingancin hadisin. Wasu malamai sun dauki hadisan mutawatirai a matsayin wani bangare na hadisai Mashurai, kamar Ibn Jama’ah, Ibnus -Salah, da An-Nawawi.