15 Yuni 2024 - 12:47
An Gudanar Da Taron Bara'a Daga Mushrikai A Saharar Arafat + Hotuna

An fara gudanar da taron barranta daga mushrikai ne mintuna kadan da suka gabata (da misalin karfe 9:00 na safe agogon Makkah, karfe 9:30 na safe agogon Tehran) a cikin saharar Arafat.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Ta hanyar halartar wannan taro mahajjatan Iran da wasu gungun alhazan da ba Iraniyawa ba sun bayyana barrantarsu da kyama ga kafirai da mushrikai, suna masu koyi da Manzon Allah (SAW).

Har ila yau, a cikin wannan taro an karanta sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi wa alhazan Baitullahil-Haram.

Aikin Hajjin bana an nuna kyama ga Amurka da Isra'ila saboda laifukan da gwamnatin sahyoniya take aikatawa na kashe kananan yara tare da goyon bayan Amurka.


الكعبة تجمعنا لدعم فلسطین