15 Yuni 2024 - 10:22
Sakon Kakakin Rundunar Al-Qassam Ga Mahajjata: An Kai Harin Guguwar Al’aqsa Ne Don Kare Masallacin Al’aqsa Harami Na Uku Mai Girma Wajen Al’ummar Musulmi

Kakakin rundunar Hamas ya bukaci alhazan Baitullahil-Haram da su tuna da ‘yan uwansu a Gaza da Palastinu a cikin wadannan kwanaki masu tsarki.

Kamfanin dillancin labaran Ahl al-Bait (AS) -Abna- ya habarta cewa, Abu Obaidah kakakin rundunar Kataib al-Qassam reshen soja na kungiyar Hamas ya bukaci alhazan Baitullahil-Haram da su yi addu'a ga 'yan uwansu al'ummar Sabirah kuma Mujahidah na Gaza da Palastinu da addu'o'in da suke da shi a lokutan da wurare masu da kuma lokacin gudanar ibadar Hajji a ciki a wadannan kwanaki.

Kamar yadda tashar Aljazeera ta fitar yana mai cewa: a yayin da mahajjata ke gudanar da aikin Hajji, muna gudanar da aikin Jihadi ne akan makiya Allah, gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila mai mamaya, a madadin al'ummar Musulmi mai girma.

Abu Ubaydah ya kara da cewa an kai harin ne da guguwar Al-Aqsa domin kare masallacin Al-Aqsa wanda yake shine Harami na uku wajen girma.

Ya kara da cewa ayyukan Hajji wata dama ce ta tunatar da biliyoyin musulmi gaskiyar fada da makiyanmu wadanda suka karya alfarmar wurin da Manzon Allah (SAW) yayi mi’iraji, suka haifar da fasadi da barna da kuma kokarin maida kasar zama ƙasar Yahudawa a kowace rana.

......