10 Yuni 2024 - 06:05
Membobi Hudu Sun Yi Murabus Daga Majalisar Ministocin Gwamnatin Kashe Yara Ta Isra’ila A Cikin Sa'o'i Uku

Bayan murabus din Gantz da Eisenkot, Haley Trooper mabiyiya jam'iyyar Gantz, ta sanar da yin murabus na karshe daga gwamnatin Netanyahu.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Smotrich Yayi Martani Game Da Murabus Ɗin Gantz Da Cewa: Wannan Shine Abin Da Sinwar, Nasrallah Da Iran Suke So.

Ministan kudi na gwamnatin Sahayoniya Bezalel Smotrich ya sanar da cewa, matakin da Benny Gantz, mamban majalisar ministocin yakin sahyoniya na yin murabus, na barin wannan majalisar, yana da nufin wargaza hadin kan kasar Isra'ila.

Da yake mayar da martani ga shawarar Gantz na yin murabus daga majalisar ministocin yakin sahyoniya, Smotrich ya ce: Hadin kai ya fi muhimmanci a cimma nasara.

Da yake jawabi Gantz, ya ce: Matakin da kuka dauka a yau yana da nufin ruguza hadin kai saboda dalilai na siyasa kuma wannan ba wani mataki bane da ya dace.

"Benny Gantz" ya yi murabus a matsayin memba na Majalisar Yakin Sahayoniya a yammacin jiya Lahadi, 10 ga Yuni, 2024.

A yayin wani taron manema labarai, ya bayyana cewa yanke shawarar barin majalisar ministocin abu ne mai sarkakiya da zafi, ya kuma ce: Netanyahu na hana samun nasara ta hakika.

Gantz ya ce: "Batun siyasa a gwamnatin Netanyahu na haifar cikas a kan hanyar da za a yanke shawarwari masu mahimmanci a yakin Gaza, kuma ainihin nasara ta hakika shie a samau damar yanto fursunoni kana ayi wani matakin siyasa".

Dangane da murabus din Gantz, Ministan Tattalin Arziki na gwamnatin Sahayoniya ya ce: Ta hanyar yin hakan ya aikata abunda Hamas da Hizbullah da Iran suke so.

Eysenkot shima ya yi murabus daga majalisar ministocin yakin Isra'ila bayan Gantz

Gadi Eisenkot, wanda ya shiga majalisar ministocin yakin Isra'ila bayan abubuwan da suka faru a ranar 7 ga Oktoba, ya sanar da yin murabus daga majalisar ministocin yakin a jiya bayan murabus din Benny Gantz.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ya sanar da cewa: "Shigowar da muka yi a majalisar ministocin ya taimaka wajen samun nasarori da dama, amma a baya-bayan nan mun shaida cewa, ba lallai ba ne matakan da ake dauka ba zasu kawo gyara ga Isra'ila".

Heli Trooper, memba a kungiyar gwamnati karkashin jagorancin Gantz, shi ma ya yi murabus daga majalisar ministocin sahyoniya tare da Gantz da Eisenkot.