10 Yuni 2024 - 03:30
Benny Guts Da Eisenkot Sun Yi Murabus Daga Majalisar Yaƙin Isra'ila.

Ana Ci Gaba Da Samun Ɓarakar Siyasa A Majalisar Ministocin Isra'ila; Benny Guts Da Eisenkot Sun Yi Murabus


Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Benny Gantz, memba a majalisar ministocin yakin Isra'ila, a hukumance ya sanar da yin murabus dinsa daga wannan majalisar tare da yin kira da a gudanar da zabe da wuri. Benny Gantz ya dauki Netanyahu a matsayin cikas ga nasara a wannan yakin.

Gadi Eisenkot, shi ma wani mamba a majalisar ministocin yakin yahudawan sahyoniya, a hukumance ya sanar da yin murabus tare da ficewa daga wannan majalisar bayan Benny Gantz!