8 Yuni 2024 - 14:09
Shahidan Harin Da Isra'ila Ta Kai Sansanin Nusairat Sun Karu Zuwa Mutum 150 + Hotunanl

Da tsakar rana ne jiragen yakin Isra'ila da dama ne masu saukar ungulu suka yi ruwan bama-bamai a sansanin Nusairat da ke tsakiyar zirin Gaza da kewaye. Ya zuwa lokacin da ake wallafa wannan rahoto, adadin shahidan sansanin "Al-Nusairat" ya karu zuwa mutane 150.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa:Ma'aikatar Lafiya ta Gaza:

Da tsakar rana ne jiragen yakin Isra'ila da dama ne masu saukar ungulu suka yi ruwan bama-bamai a sansanin Nusairat da ke tsakiyar zirin Gaza da kewaye. Ya zuwa lokacin da ake wallafa wannan rahoto, adadin shahidan sansanin "Al-Nusairat" ya karu zuwa mutane 150.

Mata da kananan yara Falasdinawa da dama ne suka yi shahada a harin da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai a tsakiyar zirin Gaza a yau. Asibitin "Shuhada al-Aqsa" baya da karfin karbar karin shahidai da wadanda suka jikkata. Saboda munanan yanayin da wasu mutanen da suka jikkata ke ciki, akwai yuwuwar karuwar yawan shahidai.