Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Sojojin Yaman sun kuma sanar da cewa sun kai hari kan jirgin Eisenhower da ke cikin tekun Bahar Maliya, amma hukumomin Amurka sun yi shiru game da hakan tare da yin kamar ba abin da ya faru!
Bayan haka, masu fafutuka a shafukan sada zumunta sun buga hotuna da aka ce tauraron dan adam na kasar Sin ne ya nada, wanda ke nuna wani babban rami a wurin saukar jiragen a kan wannan jirgin.
A cewar masana, da alama ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon ba za ta amince da kasancewar irin wadannan jiragen ba a yankin tekun Bahar Maliya daga yanzu saboda barnar da harin sojojin Yaman ke kaiwa wadannan jiragen.