Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Ma'aikatar Ilimi ta Falasdinu ta bada rahoton ce: Galibin wadannan yaran da suka yi shahada tun ranar 7 ga Oktoba, 2023 (15 ga Mihr, 1402) daliban makarantu ne da makarantun renon yara. A daidai wannan lokacin da muke ci ma dalibai 65 da sojojin mamaya suka shahadantar a yammacin gabar kogin Jordan.
Yara ne laifukan ta'addanci gwamnatin sahyoniyawan yafi shafa a zirin Gazan kuma sun tafka mummunar asara sakamakon wannan yaki. Tun farkon yakin da ake yi da zirin Gaza, dalibai ƙananan makarantu guda 620,000 da daliban manyan makarantu guda 88,000 ne aka haramta masu yin karatu sakamakon wannan yakin, kuma akasarin waɗanda su kai saura na fuskantar raunuka na tunani da na jiki.