4 Yuni 2024 - 13:23
Sojojin Yaman Sun Kai Hari Kan Sojoji Isra’ila A Tashar Ruwa Ta Eilat / Kaddamar Da Makami Mai Linzami Na "Falasdinu" A Karon Farko.

Dakarun Yaman sun kai hari tashar jiragen ruwa ta Eilat da makami mai linzami mai suna "Falasdinu".

Kamfanin dillancin labaran Ahlal-Bait (AS) - Abna – ya ruwaito maku cewa Birgediya Janar Yahya Saree kakakin rundunar sojin kasar Yaman ya sanar da kai hari da makami mai linzami kan sojojin yahudawan sahyuniya a yankunan da suka mamaye.

Kakakin Rundunar Sojin Yaman ya ce: Mun kai hari kan wata matattarar sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da ke yankin Ummur-Rashrash (tashar ruwa ta Elat) da ke kudancin Palasdinu da ta mamaye.

Ya kara da cewa dakarun kasar Yemen sun kai hari kan wannan wajen tsaron sojan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da makamai masu linzami.

Yahya Saree ya ce an kai wannan harin ne a karon farko da makami mai linzami mai suna "Falasdinu" kuma makamin ya kai daidai da inda aka harba shi.

Dukka bai ambata cikakkun bayanai dalla-dalla na wannan makami mai linzami ba.

Kakakin rundunar sojin Yaman ya jaddada cewa, za a ci gaba da kai farmakin sojojin na Yaman har sai an daina kai hare-hare a zirin Gaza tare da kawo karshen kawanyar da akaiwa al'ummar Palastinu.

A cikin 'yan watannin da suka gabata, domin nuna goyon baya ga gwagwarmayar da al'ummar Palasdinu ke yi a zirin Gaza, sojojin kasar Yemen sun kai hari kan wasu jiragen ruwa na Amurka, Birtaniya da yahudawan sahyoniya, da kan wasu jiragen ruwa da ke kan hanyarsu ta zuwa yankunan da aka mamaye a cikin tekun Red Sea da mashigar Bab al-Mandab.

Dakarun sojojin Yaman sun jajirce wajen kai farmaki kan jiragen ruwan wannan gwamnati ko kuma jiragen da ke zuwa yankunan da aka mamaye a cikin tekun bahar maliya har sai gwamnatin Isra'ila ta daina kai hare-hare a zirin Gaza.

Tun farkon hare-haren da Isra'ila ke kai wa zirin Gaza, sojojin Yamen suna kai hare-hare a yankunan da aka mamaye da makamai masu linzami iri-iri, makamai masu linzami da jiragen kunar bakin wake.