4 Yuni 2024 - 12:13
Yahudawan Sahyuniyawa Sun Kai Hari Kan Motar 'Yan Sandan Kungiyoyin Sakan Agaji | Shahidai 8 Da Jikkata Wasu Da Dama

Mayakan gwamnatin yahudawan sahyoniya sun kai hari kan wata mota 'yan sandan kungiyoyi masu zaman kansu na musamman masu kula da ayyukan jin kai a Deir al-Balah dake tsakiyar zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: A wannan harin, mutane 8 ne akasari daga jami'an tsaron Falasdinu suka yi shahada. Aikin wadannan dakaru shi ne tabbatar da tsaron kayayyakin jin kai a lokacin da ake mika su zuwa ga Gaza.

Kuma Mayakan gwamnatin mamaya sun afkawa wata motar daban a kusa da daya daga cikin matsugunan da ke da alaka da kungiyoyin kasa da kasa kusa da asibitin shahidan Al-Aqsa. A cikin wannan harin, mutane da dama, wadanda akasarinsu kananan yara ne suka jikkata, kuma an kai dukkansu asibitin shahidan Al-Aqsa.