Hujjatul Islam Wal-Muslimeen
Maliki a wata hira da ya yi da wakilin kamfanin dillancin labarai na Hauzha a
birnin Mashhad, yayin da yake nuna alhininsa dangane da kusantar zagayowar
ranar wafatin jagoran juyin juya halin Musulunci, Imam Rahil (RA) dangane da Muhimmancin
tunawa da sassan rayuwar Imam da suka bayyana ya jaddada cewa; mafi girman
siffa ta Imam Rahil (RA) ita ce yin hidimarsa da bautarsa; Imam ya kasance bawan
Allah kuma ibadarsa ce zata sa a ga duk wannan karfi da kyan gani a tattare da
shi.
Da yake bayyana cewa mu mun san masoyinmu Annabin Musulunci (SAW) a matsayin bawan Allah saboda haka, cewa matsayin bauta wani matsayi ne na musamman, sai ya bayyana cewa: A cikin sallah muna shaidawa cewa: «أَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّداً عَبْدُهُ وَ رَسُولُهُ» yana nufin a cikin sallah muna bayar da shaida akan kasancewarsa bawan Allah kuma ta fuskar ilmin Ubangiji da abunda ke boye, ya zama dole a ce shi yana halin bauta kuma bawan Allah ne shi.
Malamin manyan darussa a makarantar hauza ta Khorasan ya ci gaba da cewa: Ibada wani abu ne da yake daukar launin ubangiji idan ya kai ga kololuwarta, kuma bautar Allah gaskiya ce da ke tattare da ubangijintaka da cikakken bayyanar Ubangiji madaukaki.
Hujjatul-Islam Wal-Muslimin Maliki ya bayyana cewa aikin bauta yana sanyawa ya zamo ako da yaushe mutum yana aikata aikin Allah kuma mutanen da suke kallon hakan su yi ta mamaki akan bayyanar wannan tasiri da ke ga mutane. ya kuma yi nuni da cewa: Misalin irin wannan karfi da tasirin ibada akwai shi tattare da Imam Rahil Ibadar Imam Rahal (RA) ta kai tsororuwar da lokacin da matasa suka fahimci Imam ba shi da lafiya, sai suka je asibiti suka jeru a gefen asibitin suna rokon cewa idan zuciyar Imam ta shiga damuwa, ku ciri zuciyarmu ku sanya ta a madadin zuciyar Imam Rahil (RA) wannan ita ce bayyanar tasirin yin bauta.
Ya kara da cewa: Duk wadannan dalilai ne da ke tabbatar da cewa a cikin kogin tafiya zuwa ga Ubangiji Allah, idan mutum ya zama bawa kuma ya kai ga matsayin bauta, to tasiri da bayyanar rayuwarsa za su zama kalar ta Allah. Wato sifofi da sunayen Ubangiji su bayyana a cikinsa, don haka Ruhullah, Abdullah bawan Allah ne tsantsa kuma mai ikhlasi, wanda ya iya kutsawa da mamaye zukatan mutane.
Malamin makarantar Hauzar Khorasan ya ci gaba da cewa: kamar haka nan ne shima Annabi (SAW) ya tara mutane a kusa da shi kamar malam buɗe mana littafi a Madina, kuma wannan shi ne sakamakon bautar Manzon Allah (S.A.W) kuma alama ce ta ƙarfi da girma ga Musulunci.