26 Mayu 2024 - 21:21
An Gudanar Da Jana'izar Mahaifiyar Sayyid Hassan Nasrallah A Garin Ghabeiri

An gudanar da Rakiyar Jana'izar gawar uwa mai girma madaukakiya Hajiya Saliha "Umma Hasan" mahaifiyar babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon a garin Ghabeiri.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: kungiyar Amal da kuma al’ummar kasar Lebanon tare da dimbin mabiya addinai da na siyasa, sun gudanar da rakiyar gawar Mahaifiya mai daraja da daukaka Hajiya Saliha Ummu Hasan, mahaifiyar babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah.

A cikin wannan gagarumin taro, Sayyid Hashim Safiyuddin shugaban majalisar zartaswar kungiyar Hizbullah ya yi sallah ga gawar marigayiyar, sannan aka binne gawar wannan baiwar Allah a makabartar Al-Shahadin Ghabeiri (daya daga cikin kauyukan kasar Labanon da ke gundumar Baabda) a Lardin Jabal Lebanon.