Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Taron kuma ya kasance ne, karkashin Kulawar wakilin 'yan uwa na garin Kano, Sheikh Sunusi Abdulkadir. Wasu Muhimman dalilai da Suka bijiro yasa ba'aga Fuskar Allamah Ibraheem Zakzaky (H). Da yake Shine Babban bako a wajen amma ya kasance damu a ruhi.
Mallam Imam Yakubu, Shine Mai gabarwa, bayan bude taro da Addu'a da karatun alkur'ani, an Mike anyi wakar Salam Farmande, don girmamawa ga Imamul Hujjah (AF).
Bayan Kammala wane, aka Fara karatun yara na gwaji, daga ajin Imam Ali (As), Sannan ajin Imam Hasan dana imam Husain (As), Sannan ajin Mata Masu hadda na Sayyida Zahra (As).
An gabatar da Sha'irai bayan da Suka Kammala, Wanda Alh Mustapha G/Kaya ya Cashe Shi da Alh Bashir dandago.
Sai aka gabatar da wakilin 'yan uwa almajiran Sheikh Zakzaky (H), Dr Sunusi abdulkadir, Wanda yayi takaitaccen Jawabi, ya kuma kawo Abinda yake faruwa a Falasɗinu, Sannan aka Sanya Jawabin Jagora (H), da yaiwa Mahadda da Zuka Ziyarce Shi a gidansa dake babban birnin tarayya Abuja,
Bayan ya Kammala ne aka bada kyaututtuka, ga wasu Fitattun Mutane, Kamar Mai martaba Marigayi Sarkin Kano, Alh (Dr) Ado bayero. Da kuma Marigayi Liman waziri Murabus, Mallam Nasir Limamin Masallacin waje (Fagge). Sannan kuma 'yan uwa Maza da Mata Kamar yanda Za'a gani a hotuna, daga karshe, Dr Nura Ahmad Azare Shugaban Lajna na fudiyya ta kasa yai Jawabin godiya, aka gabatar da Sheikh Sharif Khidir Lawal Kano, ya rufe da Addu'a aka Sallami Jama'a.































