Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Daya daga cikin masu zanga-zangar da suka halarci taron ya yi kira da babbar murya cewa Kai da gwamnatin Amurka kun yi dumu-dumu da hannayenku da jinin al'ummar Gaza.
A wani bangare na taron, wani mai goyon bayan Falasdinu ya katse jawabin Austin, ya kuma ce wa gwamnatin Amurka: “Ku Kawo Karshen Kashe Mutanen Gaza. Ya Isa Hakanan, 'ya'ya nawa ne za su mutu don ku gamsu"?.
