Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: An taso da Muzaharar ne bayan idar da Sallah Juma'a a Central Mosque dake tsakiyar birnin Tarayyar Nijeriya Abuja, inda dubbanin yan'uwa Maza da mata da yara suka fito dauke da tutocin Palestine tare hotuna na irin ta'addancin da ake ma yara a ƙasar ta Falasɗin.
Muzaharar wacce aka shafe sama da awa guda ana gudanar da ita cikin tsari, tun daga Babban Masallacin na kasa har Zuwa Kasar Gadar Bega, ana slogan na Death to America da Death to Isreal inda aka fara Muzaharar lafiya duk da barazanar jami'an tsaro haka aka gama ta lafiya.
26 Ramadan, 14455
th March, 2024

























