Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, A cewar wannan rahoto, wani tsohon sojan gwamnatin Sahayoniya mai suna "Over Donyo" ya kashe kansa.
Tashar talabijin ta 12 ta gwamnatin Sahayoniya ta bayar da rahoton cewa: Kwana daya bayan binne wani soja da ya kona kansa sakamakon matsalolin tunani da yakin Gaza ya haifar a shekara ta 2014, wannan sojan da ke zaune a yankunan kudanci ya kuma gamu da tsananin kaduwa ne sakamakon aikin Soja da ya sha wahala, inda ya kashe kansa.
@abna24