Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Muhammad Al-Tamimi kwamandan kungiyar Al-Hashd Al-Shaabi ya bayyana cewa: Sojojin Al-Hashd sun aiwatar da shirin tsaro na watan Muharram tare da bada kulawar tsaro a duk wata Husseiniyya da cibiyoyin addini da wuraren da ake gudanar da tarukan Muharram.
A cewar wannan babban kwamandan kungiyar ta Al-Hashd al-Shaabi, sama da gurare 600 ne ke karkashin kulawar tsaro kai tsaye na kungiyar Al-Hashdush Shaabi domin dakile duk wani abu da ya shafi tsaro da tarukan makoki.
Ya jaddada cewa: Za a aiwatar da wannan shiri ne tare da hadin gwiwa rundunar Operation Diyala da sauran cibiyoyi masu hannu a cikin.