1- Duk wanda na zama ni shugabansa to Ali ma shugabansa ne, Ya Allah ka so wanda yake son shi, kuma ka ki wanda ya ki shi (bangaren hudubar Annabi (SAW) a Ghadirakm).
Wani Sashe Na Hudubar Manzon Allah {SAWA} A Ranar Gadir
2- Allah Ta’ala ya yi mini wahayi cewa: (Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai, Ya manzo, ka isar da abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka – dangane da Ali, yana nufin a halifancin Ali bin Abi Talib – Idan kuma ba ka aikata ba. to, ba ku isar da sakonsa ba, kuma Allah yana tsare ka daga mutane).
Wani Sashe Na Hudubar Manzon Allah {SAWA} A Ranar Gadir
3- Jama'a ban gaza wajen isar da abin da Allah Ta'ala Ya saukar zuwa gare ni ba, kuma ina bayyana muku dalilin wannan ayar: Jibrilu ya sauko zuwa gare ni sau da yawa, sa'an nan Ubangijina ya umarce ni da aminci - kuma Shi ne amincin kansa – cewa na tashi tsaye a wannan fage da sanar da duk wani baki da fari cewa: Ali binu Abi Talib dan'uwa ne, Shi ne mai zartarwa kuma magajina (ga al'ummata) kuma Imami a bayana, wanda yake da matsayin Haruna a gurina kamar yadda Haruna yake a gurin Musa, face babu wani Annabi a bayana, kuma shi ne majibincin ku, bayan Allah da ManzonSa.
Wani Sashe Na Hudubar Manzon Allah {SAWA} A Ranar Gadir
4- Kuma Allah mai albarka da daukaka ya saukar da aya daga littafinsa akan haka (ita ce): Shugabanku su ne masu bayar da zakka alhalin suna ruku'u, kuma Ali bin Abi Dalib shi ne ya tsayar da sallah, kuma ya bayar da zakka alhalin ya kasance yana ruku'u, wanda nufin Allah Ta'ala a kowane hali.
Wani Sashe Na Hudubar Manzon Allah {SAWA} A Ranar Gadir
5- To, ku sani jama'a (wannan batu ku fahimce shi kuma ku sani) cewa Allah ne ya sanya shi a matsayin waliyinku kuma limami wanda ya wajabta da'a a kan Muhajirai da Ansaru, da wadanda suka bi su da kyautatawa, a kan Bakauye da Dan Birni, da wanda ba Balarabe da Balarabe, da ’yantacce da bawa, da yaro da babba, da fari da baki, da kan duk wanda ya kadaita Allah.
Wani Sashe Na Hudubar Manzon Allah {SAWA} A Ranar Gadir
6- Hukuncinsa mai zartuwa ne a cikinku, kamar yadda maganarsa take zartacciya, ku aiwatar da umurninsa, la’ananne ne wanda ya saba masa, kuma wanda ya bi shi ya gaskata shi ya kasance mai samun rahama, don haka Allah Ya gafarta masa, da wanda ya ji daga gare shi, kuma ya bi shi.
7- Jama'a, wannan shi ne matsayi na karshe da zan tsaya a wannan fage, saboda haka ku ji kuma ku yi biyayya, kuma ku mika wuya ga umurnin (Allah) Ubangijinku, domin Allah Madaukakin Sarki ne shugabanku, kuma ubangijin ku, sannan a bayansa akwai manzonsa da Annabinsa da yake yi maku magana, sannan a bayana Ali ne shugabanku, kuma limaminku da umurnin Allah Ubangijinku, to Imamanci yana cikin zuriyarsa har ranar da zaku hadu da Allah da ManzonSa.
Wani Sashe Na Hudubar Manzon Allah {SAWA} A Ranar Gadir
8- Ya ku mutane, ku fifita shi, domin Allah ya fifita shi, kuma ku karɓe shi, domin Allah ne ya jagorantar maku da shi. Ya ku mutane, shi limami ne daga Allah, kuma Allah ba zai tuba ga duk wanda ya yi musun waliyyancinsa ba kuma ba zai gafarta masa ba, ya zama wajibi ga Allah ya yi hakan ga wanda ya saba wa umurninsa, kuma ya yi masa azabar azaba har abada abadin. Don haka ku kiyaye kada ku saba masa. Sabõda haka, za ku haɗu da wata wuta wadda makamashinta mutãne da duwãtsu ne, an yi tattalinta dõmin kãfirai.