Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (AS) - ABNA ya habarta cewa, an gudanar da taron kasa da kasa a safiyar jiya Litinin 29 ga watan Mayu shekara ta 2023 tare da halartar Ayatullah Reza Ramezani babban sakataren Majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya, taron mai taken "juyin juya halin Musulunci da al'ummar zamani da dama da kalubale" data gudana a tsakiyar harabar jami'ar Tehran. An gudanar da wannan taro ne tare da hadingwiwar majalissar Ahlul-baiti (AS) ta duniya da nufin yin bayanin irin rawar da juyin juya halin Musulunci ya taka a cikin al'ummar wannan zamani da nazari kan abubuwan da suka tabbatar da zaman lafiya da ci gaban al'umma da damar da suke da ita da kuma kalubale.

















