26 Agusta 2022 - 19:54
​Siriya: Sojojin Amurka Akalla 3 Ne Suka Ji Rauni Sandiyar Faduwar Makamin Roka A Sansaninsu

Rahotannin sun bayyana cewa akalla sojojin Amurka 3 ne aka tabbatar da cewa sun ji rauni sanadiyyar faduwa makaman rokoki a kan sansanunsu dake arewacin kasar Siriya da Amurka ta mamaye.

Kamfanin dillancin labaran SANA na gwamnatin kasar Siriya ya bayyana cewa rokokin sun fada ne a kan sansanin sojojin Amurka da ke kusa da rijiyar mai mai suna Al-Umar da kuma Koniko a wajen birnin Dayr-Al-Zawr.

SANA ya nakalto kamfanin dillancin labaran reuters na cewa sojojin amurka akalla ne aka tabbatar da cewa sun ji ranuka ba masu tsanani ba sanadiyyar fashewar rokokin.

Labarin ya kara da cewa sojojin Amurka sun killace yankin daga shiga ko fita, sannan an ga jiragen yakin Amurka masu saukar ungulu suna ta shawagi a yankin. Sannan hare-hare rokokin sun zon ne bayan da jiragen yakin Amurka suka kai hare-hare da jiragen sama a safiyar yau Alhamis a birnin Dayr-Al-Zuwr

342/