A lokacin ‘yan Rohingyas kimanin 750,000 ne sukayi kaura daga jihar Rakhine zuwa iyakar Bangaladesh, domin gujewa kisan kiyashin sojojin na Myammar.
A ranar 25 ne ga watan Agustan 2017 ne dakarun Myanmar suka kone kauyukan ‘yan Rohingya fiye 300, abinda ya tilastawa ‘yan kabilar wadanda galibi Musulmi kwarara zuwa iyakar Bangladesh.
Sansanin na ‘yan Rohingyas dake kudu maso gabashin Bangaladesh shi ne wani sansani na ‘yan gudun hijira mafi girma a duniya.