Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, na mai zargin kasashen da kawo cikas ga sha’anin tsaron kasarsa.
Kafin nan ministan harkokin wajen Turkiyyar, Mevlüt Cavusoglu, ya ce, yana fatan kasashen zasu nuna da gaske su ke.
Turkiyya dai na son kasashen su kawo karshen abunda take kira goyan bayan da su ke baiwa ‘yan PKK, da kuma dage mata takunkumin sayar mata makamai da aka kakaba mata a 2019 bayan matakin sojin data dauka kan Kurdawan Siriya.
342/