23 Mayu 2022 - 16:35
​Iraki: Mayakan Hashdu Sun Kashe ‘Yan Ta’addan ISIS Da Dama A Arewacin Kasar

Dakarun gamayyar kungiyoyi masu yaki da ‘yan ta’adda ta kungiyar ISIS a Kasar Iraki, wadanda aka fi sani da Hashdushaabi sun cilla makaman atilary kan wani sansanin mayakan na ISIS a arewacin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A wani bayanin da gamayyar mayakan na Hashdu ya fitar a safiyar yau Litinin, ya bayyana cewa rundunarsa ta 22 ce ta cilla makaman na atilari kan sansanin ‘yayan wannan kungiyar a tsibirin Al-aith da ke cikin lardin salahuddin.

Dakarun sun kara da cewa irakawa kada su damu matukar mayakan Hashu suna nan, to ISIS ba zata sake tasowa a kasar Iraki ba. Labarin ya kara da cewa an kashe mayakan na ISIS da dama wasu da dama kuma sun ji rauni.

Har’ila yau a wani labarin majiyar jami’an tsaron kasar ta Iraki ta bayyana cewa a jiya Lahadi, sun kama mayakan na ISIS 21 a larduna daban-daban a kasar. Daga ciki har da wasu shuwagabanninsu. Daga landunan Ambar, Kirkuk Niniwa da Kuma Diyala. Banda haka a jiya Lahadin, mayakan sama na sojojin kasar ta Iraki sun kashe mayakan na Isis ta sama a wani wuri a lardin Salahuddin.

342/