18 Mayu 2022 - 19:34
​Ma'aikatar tsaron Isra'ila ta sanar da bayar da agaji ga Ukraine

A yau Laraba, ma'aikatar tsaron Isra'ila ta sanar da aikewa da agaji ga kungiyoyin agajin gaggawa da kungiyoyin fararen hula a Ukraine, da suka hada da kwalkwali 2,000 da rigunan kariya 500.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ma'aikatar ta bayyana cewa, bisa ga umarnin ministan tsaro Benny Gantz, ma'aikatar tsaron a yau 18 ga Mayu, 2022, ta aike da kwalkwali 2,000 da riguna na kariya 500 ga kungiyoyin agajin gaggawa da na farar hula a Ukraine.

Wannan mataki dai ya kara tabbatar da zargin da ake yi kan cewa Isra'ila tana daga cikin wadanda suke ingiza gwamnatin Ukraine tun daga farko, lamarin da ya kai ga barkewar yaki tsakaninta da Rasha.

342/