17 Mayu 2022 - 19:29
​Lebanon: An Fara Fitar Da Sakamakon Zaben Majalisar Dokokin Kasar

Ma’aikatar cikin gida na kasar Lebanon ta fara bada sakamakon zaben ‘Yan Majalisar dokokin kasar Lebanon wanda aka gudanar a ranar Lahadi 15 ga watan Mayun da mukeciki.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Bissam Maulawi ministan harkokin cikin gida na kasar ya bada sakamakon zabe a larduna 12 cikin 15 da ake da su a kasar, ya kuma bayyana cewa wannan bas hi ne sakamakon zaben na karshe ba tunda har yanzun ba’a kammala arga wasu kuri’un ba.

Majalisar dokokin kasar Lebanon dai tana da kujeru 128 wadanda za’a zabi masu cike su daga jam’iyyu da kungiyoyi daban daban na kasar.

Jaridar Al-Akhabar ta kasar ta bayyana cewa sakamakon zaben a shiyoyin zabe 12 daga cikin 15 da ake da su a kasar sun nuna cewa.

Hazbullah ta sami kujeru 12, Kungiyar Amal ta 9, sai Tayyar watan Al-hur ta samu kujeru 17, sannan jam’iyyar Marada 2, sai Kuwaatul Lubnaniyya ta sami kujeru 19, sannan Mustakabal ta sami kujeru 26 , kata’ib lebnaniyya ta tashi da kujeru 2, Tashanq 2, jam’iyyar gurguzu 7, wadaniyyin Al-Ahrar kuma 1.

Kungun kawancen jam’iyyu wadanda suka sami kujeru fiye 64 daga 128 da ake da su sune zasu sami rinjaye a majalisar dokokin kasar.

342/