8 Mayu 2022 - 15:09
Hamas Ta Sha Alwashin Yi Wa Isra’ila Ruwan Rokoki, Muddin Ta Kuskura Kashe Mata Wani Shugaba

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi gargadin cewa za ta wargaza wasu garuruwan da Isra'ila ta mamaye kurmus, idan har gwamnatin Tel Aviv ta dauki mataki kan barazanar da take yi na kashe wani daga cikin shugabannin kungiyar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A cewar gidan talabijin din al-Mayadeen na kasar Labanon, Hamas ta shaidawa masu shiga tsakani na Masar cewa ba za ta rufe ido akan barazanar da gwamnatin Isra'ila ke yi na kashe shugabanninta ba.

Kafofin yada labaran Isra'ila sun rawaito bangarori da dama dake kiraye-kirayen kashe manyan jami'an Hamas, wato Yaha Sinwar, shugaban 'yan gwagwarmaya a zirin Gaza, bayan harin wuka da aka kai a tsakiyar birnin Elad a ranar Alhamis data gabata.

Mamba mai tsattsauran ra'ayi na Knesset Itamar Ben-Gvir ya yi kiran da a wargaza gidan Sinwar, da makami mai linzami.

Kasar Masar dake zama ‘yar shiga stakani a rikicin Falasdinu da Isra’ila, ta gargadi mahukuntan Tel-Aviv, akan daukar irin wannan matakin na kisan wani shugaban kungiyoyin gwagwarmayar falasnawa Hamas ko Jihad Islamic, wanda ke nufin shelanta yakin da ba’a san ranar karshensa ba.

342/