6 Mayu 2022 - 18:51
Rikici Na Kara Kamari Tsakanin Rasha Da Isra’ila Kan Taimakawa Ukrain

Isra’ila ta bayyana taimakon kayan yaki da ta aikewa kasar ukrain domin karfafa sojojinta amsa bukatar da shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar mata ne, wanda hakan ya kawo rikice mai tsanani tsakanin Isra’la da kasar Rasha.

A makon jiya ne Isra’ila ta aike da babban kwamandan sojinta zuwa sansanin sojin sama na Ramstein a kasar Jamus domin halartar taron da Amurka ta kira kan yadda za’a aikewa da kasar Ukrain daukin makamaki,

Wani jami’in Isra’ila ya bayyana cewa ba zasu aike da manyan makamai ko naurorin zamani ba kamar na’urar kakkabo makamai masu linzami ba, amma dai suna duba yi yuwar bada tallafin kayan yaki da baza su haifar da rikici tsakaninta da kasar rasha ba,

Rasha ta kaddamar da harin soji ne kan kasar Ukrain a ranar 24 ga watan Fabareru da nufin hana kasar hadewa da dakarun tsaro na Nato,

A watan jiya rasha ta gargadi Isra’ila na mayar martani mai zafi idan ta kuskura ta aike da kayayyakin soja zuwa kasar Ukrain , kuma wannan yanazuwa ne bayan da ministan yaki na isra’ila Banny Gantz ya sanar da cewa za su aike da agajin kayan yaki ga kasar Ukrain.

342/