Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Cikakken Jawabin Nasa Na Ranar Kudus Ta Duniya Shekara Ta 2022m Shi Ne Kamar Haka
- Hakika Halatar mutane a Jerin Gwanon ranar Qudus ya kasance abin al'ajabin gaske.
- Wannan yunkuri da halartar mutane aiki ne mai girma da albarka domin kare Qudus.
- Wadanda suke kare Falasdinu a birnin Quds a yau za su kara samun karfin gwiwa ta hanyar taruka na nuna goyon bayan al'ummomi, da ake gudanarwa a ranar Kudus, kuma za a samu sakamako mai mahimmanci dangane da hakan.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi tsokaci kan yadda mutane suka halarci tattakin ranar Kudus, inda ya yi bayani da harshen larabci, wanda aka fassara kamar haka;
Bismillahir Rahmanir Rahiim
- ina mai yin Sallama ga dukkan 'yan uwa musulmi a fadin duniya! Sallama ga matasan duniyar musulmi! Gaisuwa da jinjina ga jajirtattun matasan Palastinu masu kishi da dukkan al'ummar Palastinu. Ranar Kudus ta sake ta sake zagayowa wanda ya zamo Kudus tana kira ne ga dukkan musulmin duniya.
- Maganar gaskiya matukar dai gwamnatin sahyoniyawan masu kwace da muggan laifuka ta mamaye birnin Qudus, to ya kamata a ce duk ranakun shekara a dauke su a matsayin ranar Kudus. Kudus mai tsarki ita ce zuciyar Palastinu, kuma a dukkan fadin kasar da aka kwace tun daga teku har zuwa rafi, dukan sa yana cikin kasar Qudus ne. Al'ummar Palastinu suna kara nunawa a kowace rana cewa sun tsaya tsayin daka kuma suna yin adawa da azzalumai ta hanyar jajircewa mara misaltuwa. Matasan sun zama garkuwar kare Falasdinu ta hanyar ayyukan sadaukar da kai, kuma suna shelanta samuwar wata makomar nasara ta daban nan gaba.
- Muna gudanar da ranar Qudus ta wannan shekara ne tare da duk abin da ke sanar da sabbin daidaito na yau da gobe da ka iya samuwa a kasar Falasdinu. A yau, "rashin nasara" ya maye gurbin "rundunar sojojin sahyoniyawa da su ke ganin ba za a iya cin nasara akan su ba" a Palastinu da kuma yammacin Asiya. A yau, an tilasta wa sojojin masu aikata laifuka su mayar da tsarinsu na kai farmaki zuwa ga na kare kai.
- A yau a fagen siyasa, babbar mai goyon bayan gwamnatin ‘yan mamaya, Amurka, ta sha kashi iri-iri: shan kaye a yakin Afganistan, shan kashi a cikin manufofin matsin lamba kan Iran Musulunci, shan kashi a kan manyan kasashen Asiya, gazawa a cikin kula da tattalin arzikin duniya, gazawar gudanarwa na cikin gidanta, wanan al'amarin ya haifar da baraka mai zurfi a cikin ikon maulkin Amurka.
- Gwamnatin masu cin zarafi acikin fagage biyu na siyasa da na soja, tana cike da rudani da matsaloli; sannan Tsohon mai aiwatar da hukuncin kisa kuma mai laifi wanda ya kasance shugaban gwamnatin a da ya shiga cikin kwandon sharar tarihi ne bayan waki'ar Saif al-Quds, kuma magajinsa a yau yana jiran a ko wace sa'a sadda shima zai hadu da nasa kaifin.
- Motsin da akayi A Jinin ya sanya gwamnatin sahyoniya ta haukace. Shekaru 20 da suka gabata, a matsayin mayar da martani ga kisan da aka yi wa Yahudawan sahyoniyawan da dama a Naharia, gwamnatin 'yan mamaya sun kashe mutane 200 a sansanin Jinin domin magance wannan matsalar har abada!
- Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa kusan kashi 70 cikin 100 na Falasdinawa a yankuna na 48 da na 68 da kuma sansanonin kasashen ketare suna karfafawa shugabannin Falasdinawa gwiwa wajen kaddamar da hare-haren soji kan gwamnatin mamaya. Wannan lamari ne mai mahimmanci; Domin kuwa hakan na nufin cikakken shirin Falasdinawa na tunkarar gwamnatin 'yan ta'adda, kuma hakan yana sakar hannun kungiyoyin mujahidai da su dauki mataki a duk lokacin da suka ga ya dace.
- Yunkurin jihadi na al'ummar Palastinu a yankunan arewaci da kudancin kasashe 48, sannan kuma an gudanar da gagarumin jerin gwano a Jordan da gabashin birnin Kudus da kuma kariyar da matasan Palastinawa suke yi kan masallacin Al-Aqsa, da atisayen tsaro da aka gudanar a Gaza ya nuna cewa daukacin kasasen Falasdinu sun zama fagen gwagwarmaya. Wanda yake Yanzu al'ummar Palastinu sun hada kai wajen ci gaba da jihadi.
- Wadannan abubuwan da suka faru da kuma abubuwan da suka faru a kasar Falasdinu a cikin 'yan shekarun nan, su ne hatimin soke duk wani shiri na yin sulhu da makiya yahudawan sahyoniya, domin ya nuna ba za a iya aiwatar da wani shiri game da Palastinu ba, ko kuma wani shiri da ya sabawa ra'ayin ma'abotanta wato Palasdinawa ba; Wannan yana nufin cewa, an soke duk wasu yarjejeniyoyin da aka yi a baya, kamar Oslo, ko shirin ƙasashen Larabawa, ko yarjejeniyar karni, ko kuma abubuwan yarjejeniyar wulakanci na baya-bayan nan dukkan su sun lalace ba karabbu bane.
- Tabbas gwamnatin Sahayoniyya duk da cewa ba ta da numfashi, tana ci gaba da laifukan da take aikatawa tare da kashe wadanda ake zalunta da makami; Tana kashe mata da yara da manya da matasa marasa makami, dauri da azabtarwa, lalata gidaje, lalata gonaki da dukiyoyi; Amma makaryata masu neman hakkin bil adama a Turai da Amurka, wadanda suka fara hayagaga a lamarin Ukraine, sun yi shiru abunsu akan wannan aika-aikar da ake yi a Falasdinu, ba wai suna kare wadanda ake zalunta ba, a’a suna ma taimakawa kyarkecin da yake shan jini.
- Wannan wani babban darasi ne a cikin lamurran da suka shafi duniyar musulmi wanda yake maja gabansu shine lamarin Palastinu, wanda ya zamo ba za’a iya dogaro da wadannan kasashe masu nuna wariyar launin fata da nun kiyayya ba, kawai abuda aka iya magance matsalolin duniyar Musulunci shine Karfin gwagwarmawa wanda ya samo asali daga koyarwar kur’ani mai tsarki da kuma dokokin Musulunci, wanda ya zamo mafi girmansu matsalar Palastinu.
Samuwar gwagwarmaya a yankin yammacin Asiya ya kasance al'amari mafi albarka a yankin cikin 'yan shekarun nan. Wannan tsayin daka shine ya tsarkake yankunan Lebanon da suka mamaye daga kazantar sahyoniyawan; kuma shiya fitar da Iraki daga makogwaron Amurka; An ceto Iraki daga ISIS; Kuma ya taimaka wa masu tsaron Siriya kan shirye-shiryen Amurka.
Lamarin gwagwarmaya yana yakar ta'addancin kasa da kasa, yana taimakawa al'ummar kasar Yemen masu juriya a yakin da aka dora musu, suna gwagwarmaya da wanzuwar 'yan mamaya na sahyoniyawan Palastinu, tare dafatan samun nasarar Ubangiji zasu durkusar da su tare da kokarin mujahidai, lamarin Qudus da Falasdinu sannu ahankali zai zama abun tunanin dukkan jama'a a duniya.
Ya ku Palastinawa, matasa masu sadaukar da kai a gabar yammacin kogin Jordan da kuma kasashen 1948, ku ne mayakan da zaku yaki sansanin Jenin, da ku Mujahiddin Quds da Gaza, da ku mazauna sansanonin Falasdinawa da ke wajen Palastinu, kun kasance bangarori ne mai muhimmanci ga motsin gwagwagrmaya.
- Ina gaisuwa agareku! Ku Tsaya Kyam kuma ku sani cewa:
«اِنَّ اللَّهَ یُدافِعُ عَنِ الَّذِینَ آمَنوا» و «لَئِن صَبَرتُم لَهُوَ خَیرٌ لِلصّابِرین» و «وَ اِن تَصبِروا وَ تَتَّقوا فَاِنَّ ذٰلِکَ مِن عَزمِ الاُمور» و «سَلامٌ عَلَیکُم بِما صَبَرتُم فَنِعمَ عُقبَى الدّار».
- Jamhuriyar Musulunci ta Iran mai goyon bayan kungiyar gwagwarmaya ce; Mai goyon bayan gwagwarmayar Palasdinawa ne; Kullum muna fadin haka kuma mun yi aiki da shi kuma mun dage dangane da shi.
- Mun yi Allah wadai da yunkurin yaudara na "sabun alaka" da manufar "Zamowa abu daya".
- Cewa wasu gwamnatocin kasashen Larabawa sun shaidawa Amurka cewa ta gaggauta warware matsalar Palastinu, idan har suna nufi da wanna maganar ta suya zamo kafin fitarsu daga wannan yankin su kawar da duk wani yunkuri da zai kawo rashin kafuwar gwamnatin 'yan ta'adda kafin ficewa daga yankin, to zai zamo abu na farko sun ci amana tare da haifar da abun kunya ga kasashen Larabawa, na biyu. sun zamo kaskantattu, domin makaho ba zai iya zama jagoran makaho ba!
Daga karshe ina jinjina ga ruhin shahidan Palastinawa; Ina girmama iyalansu masu hakuri; uma ina gaisuwa ga fursunonin Palasdinawa da fursunonin da suka yi tsayin daka da kwakkwaran manufa; Ina mika hannu da kungiyoyin Falasdinawa masu tsayin daka, wadanda suka dauki wani muhimmin bangare na wannan babban nauyi; Kuma ina kira ga al’ummar musulmi musamman matasa da su shiga wannan fage na daukaka da daraja.
342/