Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Yace idan muna Magana akan Iran zamu iya fahimtar cewa za’a iya samar da makwafin kayayyakin kasashen turai da ake amfani da shi a kasar,musamman kayayyakin da suka shafi kula dalafiya da ake amfani dasu yau da kullum
Wannan yana zuwa ne adai dai lokacin da shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya ce takunkumin da kasashen turai suka kakabawa kasarsa bai yi nasara ba, musamman kokarin da suke yi wajen durkusar da tsarin bankuna na kasar
Yace takunkumin da aka kakaba mata ba zai tafi haka nan ba tare da tasirinsa ya koma kan kasashen turai ba, domin a baya bayan nan dai kasashen turai irinsu birtaniya da Jamus sun kai kololuwar hauhawan farashin kayayyaki da ba’a taba gani ba , domin takunkumin da aka kakabawa Rasha ya kara ruruta matsalar tsadar makamashi da rashin aikin yi da tsadar rayuwa.
342/